Gwamnan Katsina: Ku Tashi Tsaye Ku Kare Kan Ku Daga Hare-Haren ’Yan Bindiga

Gwamnan Katsina: Ku Tashi Tsaye Ku Kare Kan Ku Daga Hare-Haren ’Yan Bindiga

  • Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina, ya shawarci jama'ar jiharsa da su tashi su kare kawunansu daga hare-haren 'yan bindiga
  • Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa za ta ba kowanne gari duk wata gudunmawa da yake bukata wajen yin hakan ta hanyar da ta dace
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da makarantun Islamiyya guda uku da wani ya gina a Malumfashi da Mani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bukaci al’ummar jihar da su jajirce wajen kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga da ke kai wa garuruwansu hari.

Ya bayar da wannan umarni ne a wajen kaddamar da wasu makarantun Islamiyya guda uku da wani mai taimako, Alhaji Abubakar Dardisu ya gina a Yammama da ke kananan hukumomin Malumfashi da Mani a jihar.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari sun jawo za a binciki inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr

Gwamnan Katsina ya umurci mutanen jiharsa su kare kansu daga ‘yan bindiga.
Gwamnan Katsina ya umurci mutanen jiharsa su kare kansu daga ‘yan bindiga. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Sannan gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatin sa za ta bayar da tallafin da ake bukata ga al’ummomin domin kare su da kuma jagorantar su ta hanyar da ta dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko a sakon shi na sabuwar shekara, sai da Gwamna Radda ya nemi al'ummar jihar da su taimakawa gwamnati wajen yaki da 'yan bindiga a jihar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An karrama iyayen Radda da Sarkin Katsina

Ya kuma yabawa Alhaji Dardisu bisa yadda ya sadaukar da dukiyarsa domin daukaka kalmar Allah, tare da neman mazauna garuruwan da su yi amfani da makarantun yadda ya kamata.

Makarantar Islamiyya da aka gina a ’Yan Mama an sanya wa sunan marigayi mahaifin gwamnan mai suna Bare-bari Umaru Radda, Leadership ta ruwaito.

Wadda ke Muduru an sa mata sunan mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u yayin da ta Mani kuma aka saka wa sunan Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir.

Kara karanta wannan

Daliba a Adamawa ta dauki ranta saboda saurayinta ya rabu da ita

Masari ne ya fara cewa mutane su kare kansu a Katsina

A shekarar 2021, cikin watan Agusta, tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yi kira ga al'ummar jihar da su mallaki makamai don kare kansu daga 'yan bindiga.

Legit Hausa ta ruwaito a wancan lokacin cewa, Masari ya yi wannan kiran ne lokacin da ya gana da iyalan mutum 10 da jami'an kwastom suka kashe a jihar.

A lokacin Masari ya yi nuni da cewa babu dalilin da zai sa a kyale 'yan bindiga suna mallakar bindigogi suna kashe mutane, ace su ma mutanen ba za su mallaki bindiga don kare kansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.