Gwamnan Katsina: Ku ma ku sayi bindiga ku kare kanku daga 'yan bindiga

Gwamnan Katsina: Ku ma ku sayi bindiga ku kare kanku daga 'yan bindiga

  • Gwamna Masari na jihar Katsina ya shaida wa jama'arsa cewa, kowa ya mallaki bindiga don yakar barayi
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi wajen jajantawa iyalan wasu mutane 10 da suka mutu sanadiyyar jami'an kwastam
  • Gwamnan ya ce, tunda 'yan bindiga na iya sayen bindiga su aikata ta'addanci, to 'yan kasa ma za su iya saye don kare kai

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke da yawan 'yan bindiga da su mallaki makamai su kare kansu daga ta'addanci.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai ga gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, wanda Daily Trust ta samu.

Kara karanta wannan

Babu Wasu Yan Bindiga da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Zargi Wasu Mutane a Jiharsa

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su mika wuya ga 'yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kare kansu ba, lura da cewa tsaro aikin kowa ne.

Kisan Jibia: Masari ya ce 'yankin kowa ya dauki makami don kare kansa
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Channels Tv ta ruwaito gwamnan na cewa:

"Dole ne dukkan mu mu tashi tsaye don tunkarar kalubalen rashin tsaro, kada mu zauna mu kalli wasu mutane suna sayen bindigogi suna kai hari a gidajen mu, mu ma ya kamata mu sayi bindigogin mu kare kan mu."

Meye gwamnati ke yi game da mutuwar mutane 10 sanadiyyar jami'an kwastam?

Legit Hausa ta gano Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a garin Jibia ranar Talata 17 ga watan Agusta, lokacin da ya kai ziyarar jajantawa kan rasuwar mutane 10 da wasu jami’an hukumar kwastam ta Najeriya suka yi sanadiyya a ranar Litinin yayin tuki a kan aiki.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Da yake magana game da mutuwar mutanen 10, Gwamna Masari ya tabbatar wa mutane cewa gwamnati tana bin dukkan matakan da suka dace na shari’a don neman hakkin iyalan mamatan, da kuma wadanda suka sami raunuka daban-daban.

Ya kara da cewa tuni aka tuntubi masana harkar shari’a don ba da shawara kan hanyar da za a bi don tabbatar da gaggauta warware matsalar.

Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu

A wani labarin, Majalisar Malamai/Dattawa ta Jihar Filato ta yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos da kada su kai farmaki kan kowa don daukar fansa kan kisan da aka yi wa musulmai a kan hanyar Gada-biyu - Rukuba, cikin Karamar Hukumar Jos ta Jihar Filato.

An kashe wasu Fulani matafiya musulmai a ranar Asabar a kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci wani hidiman addini a Bauchi, an kai musu hari inda aka kashe sama da 20, mutane da yawa sun ji rauni kuma kusan 10 sun bace.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

A rahoton Daily Trust, ta ce wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya ce:

"Musulunci bai goyon bayan tashin hankali saboda haka bai kamata a kai hari ko kashe wani da sunan daukar fansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: