Shiriya daga Allah: Babban fasto ya karbi musulunci a jihar Ebonyi bayan yayi mafarki

Shiriya daga Allah: Babban fasto ya karbi musulunci a jihar Ebonyi bayan yayi mafarki

- Wani babban fasto a jihar Ebonyi ya karbi musulunci bayan yayi mafarki

- Faston dai ya bayyana cewa ba kudi ne suka sa ya karbi musulunci ba

- Yanzu haka Faston ya dukufa wajen yin wa'aza domin daukaka kalmar Allah

Wani babban faston da kawo yanzu ba'a bayyana sunan sa ba daga jihar Ebonyi ya karbi kalmar shahada kuma tuni har ya soma shiga kauyuka yana wa'azi domin daukaka kalmar Allah.

Shiriya daga Allah: Babban fasto ya karbi musulunci a jihar Ebonyi bayan yayi mafarki
Shiriya daga Allah: Babban fasto ya karbi musulunci a jihar Ebonyi bayan yayi mafarki

KU KARANTA: Shawata ga mata masu son shiga harkar fim - Fati Shu'uma

Shi dai faston wanda faifan bidiyon sa ya rika yawo a kafafen sadarwar zamani ya bayyana cewa ko kusa shigar sa musulunci bata da alaka da kudi ko wani abun duniya domin kuwa iyayen sa masu kudi ne.

Legit.ng ta samu cewa faston dai ya bayyana cewa ya yanke shawarar ya shiga addinin musuluncin ne bayan yayi mafarkin da ya ratsa masa zuciya inda a ciki aka umurce shi da ya shiga musuluncin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel