Hassan da Abdullahi: Kotu ta yankewa malaman Islamiyya biyu hukuncin daurin shekaru 22

Hassan da Abdullahi: Kotu ta yankewa malaman Islamiyya biyu hukuncin daurin shekaru 22

Wata babbar kotun majistare da ke Minna, babban birnin jihar Neja, ta zartar da hukuncin daurin shekaru 22 a kan wasu malaman Islamiyya biyu; Hassan Bilyaminu da Abdullahi Bilyaminu.

An gurfanar da malaman biyu 'yan uwan juna a gaban kotu bisa tuhumarsu da aikata fyade a a kan kananan yara guda hudu da ke karatu makarantar Islamiyyarsu.

Babbar alkaliyar kotun, Hauwa Baba Yusuf, ta yanke hukunci a kan tuhuma biyu; cin zarafin kanan yara mata da rashin da'a, da ake yi wa Malaman.

A makon jiya ne rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi bajakolin malaman biyu; Bilyaminu, mai shekaru 25 da Abdullahi, mai shekaru 23, wadanda dukkansu malamai ne a tsangayar Mallam Bilya da ke Tudun Natsira Maitumbi.

"Ana zargin Malaman da aikata fyade da kuma saka yatsa a al'aurar wasu dalibansu mata da shekarunsu basu wuce 6 - 11 ba. Su na kiran daliban zuwa dakinsu domin aikata hakan.

"A yayin da su ke amsa tambayoyi, Malaman sun amsa laifinsu," kamar yadda rundunar 'yan sanda ta bayyana.

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja Bello Mohammed, ya bayyana cewa an tanadi hukuncin laifukan da Malaman suka aikata a karkashin sashe na 285 na kundin 'penal code' da sashe na 19 (2) na kundin hakkin yara na jihar Neja da aka samar a shekarar 2010.

Hassan da Abdullahi: Kotu ta yankewa malaman Islamiyya biyu hukuncin daurin shekaru 22
Hassan da Abdullahi: Kotu ta yankewa malaman Islamiyya biyu hukuncin daurin shekaru 22
Asali: Twitter

Wani bangare na tuhumar da ake yi mu su, kamar yadda dan sanda mai gabatar da kara ya karanta a gaban kotu, na cewa; "a ranar 2 ga watan Agusta, 2020, wani mutum mai suna Lawal Idris da ke zaune a yankin Maitumbi a garin Minna ya wakilci sauran mutane uku wajen shigar da korafi a kanku.

DUBA WANNAN: Babu ruwan Buhari: Masari ya fadi ma su laifi a matsalar rashin tsaro a Katsina

"A cikin korafinsu, an zargeku; Hassan Bilyaminu Da Abdullahi Bilyaminu, da yaudarar wasu yara mata 4 da ke karatu a makarantar Islamiyyarku tare da shigar dasu dakinku inda ku ka dinga saka yatsa a gabansu kuna cin zarafinsu daya bayan daya.

"Yayin da jami'an rundunar 'yan sanda ke tuhumarku, kun amsa cewa kun aikata laifin, a saboda aka gurfanar da ku bisa zarginku da aikata kaifukan da aka ambata."

Malaman biyu sun amsa laifinsu tare da neman sassauci a zartar da hukuncin da doka ta tanada a kansu, inda su ka bayyana cewa rudin shedai ne ya kaisu ga aikata hakan.

Da ta ke karanta hukuncin da kotun ta yanke; Jastis Hauwa ta bayyana cewa; "kun nuna tantsar rashin da'a, kun aikata laifin da har abada zai ci gaba da kona zukatan wadannan kananan yara da iyayensu.

"Jama'a dole su cigaba da yin mamakin wanne irin dadi mutane irinku ke ji daga cin zarafin kananan yara.

"Wannan abu ya yi yawa, dole akwai wani abu a kasa dangane da wannan annobar fyade a kan kananan yara," a cewarta.

A karshe, ta bayyana cewa kotu ta yanke mu su hukuncin daurin shekaru 22 a gidan yari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng