Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Ta'addan da Ya Halaka Nabeeha, Bayanai Sun Fito

Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Ta'addan da Ya Halaka Nabeeha, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke wani ƙasurgumin ɗan ta'adda a jihar Kaduna
  • Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa ɗan ta'addan ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka sace tare da halaka Nabeeha da wasu mutane daban
  • A cewar kakakin an cafke ɗan ta'addan ne a wani otal da ke Tafa bayan samun bayanan sirri kan motsinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya, sun cafke wani ɗan ta'adda mai suna Bello Mohammed, a jihar Kaduna.

Ƴan sandan sun cafke Bello ne mai shekara 28 a duniya wanda ya fito daga jihar Zamfara, a ranar Asabar 20 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke yan ta'adda 10 tare da cafke kasurgumin shugaban yan bindiga

Yan sanda sun cafke dan ta'adda a Kaduna
Yan sanda sun cafke dan ta'addan da ke da hannu a kisan Nabeeha Hoto: @PoliceNG
Asali: UGC

Ƴan sandan sun kuma halaka ƴan bindiga biyar ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Mai Gemu (Godara) tare da lalata sansaninsu da ke a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairun 2024.

Kakakin ya bayyana cewa DPO na ƴan sandan Tafa ne ya jagoranci wata tawaga wacce ta kai samame a wani otal da ke Tafa, bayan samun bayanin sirri kan motsin ɗan ta'addan.

A ina aka cafke ɗan ta'addan?

Ya bayyana cewa an cafke Bello ɗauke da tsabar kuɗi har N2.25m a tattare da shi wanda ake tunanin kuɗin da ya samu ne sakamakon amsar kuɗin fansa kan mutanen da ya sace a yankin.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun badda kama sun halaka jami'an yan sanda a Arewa

"Wanda ake zargin, a lokacin da ake tuhumarsa ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da suka ɗauke iyalan Barista Ariyo a Bwari, birnin tarayya Abuja, a ranar 2 ga watan Janairun 2024, inda suka halaka wasu daga ciki da suka haɗa da Nabeeha, ɗiyar lauyan a ranar 13 ga watan Janairu a sansaninsu da ke Kaduna."
"Wanda ake zargin ya kuma yi ƙoƙarin bayar da cin hancin N1m ga DPO ɗin wanda ya ƙi karɓa inda ya gudanar da aikinsa yadda ya dace."

Sanarwar ta ƙara da cewa Sufeto-Janar na ƴan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya umarci da a miƙa wanda ake zargin a hannun rundunar DFI-IRT a Abuja domin cigaba da gudanar da bincike.

Ƴan Sanda Sun Halaka Ɗan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar ta samu nasarar haƙaka wani ɗan bindiga a yankin Dandume da ke jihar.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe manyan ƴan bindiga 3 yayin musayar wuta a dajin iyakar Abuja da Kaduna

Ƴan sandan sun sheƙe ɗan bindigan ne bayan tawagarsa sun yi yunƙurin yin garkuwa da mutane a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng