Yan Bindiga Sun Badda Kama Sun Halaka Jami'an Yan Sanda a Arewa

Yan Bindiga Sun Badda Kama Sun Halaka Jami'an Yan Sanda a Arewa

  • Ƴan bindiga sun badda kama sun halaka jami'an ƴan sanda mutum biyu a wani sabon hari a jihar Katsina
  • Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sandan ne a yayin da suke tsaka da aikinsu a hanyar Jibia zuwa Batsari
  • A yayin harin ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da bindigogin jami'an ƴan sanda bayan sun halaka su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga da suka yi sanya kayan mata, sun kai hari a wani shingen bincike na ƴan sanda da ke kan hanyar Jibia zuwa Batsari a Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan bindigan a yayin harin sun kashe sufeto biyu a ƙauyen Gurbin Magarya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nemi makudan kudin fansa kan mutum 31 da suka sace a Arewa, sun tura da sako

Yan bindiga sun halaka yan sanda a Katsina
Yan bindiga sun halaka yan sanda a jihar Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Maharan waɗanda ake zargin ƴan bindiga ne, sun gudu da bindigogin jami’an ƴan sandan, inda suka bar motar da suke aiki da ita da kuma hayaki mai sa hawaye a wurin da lamarin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani majiyar tsaro da ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Juma'a, inda ya ce an kai harin ne a ranar Alhamis, inda ya ce wadanda harin ya rutsa da su ƴan sandan haɗin gwiwa ne na sintiri a kan iyaka.

Majiyar ta ƙara da cewa an kai gawarwakin ƴan sandan zuwa babban asibitin Katsina.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da bayin Allah

A wani lamari makamancin haka, da sanyin safiyar Juma’a ne wasu ƴan bindiga da dama sun kai hari a ƙauyen Gangara da ke ƙaramar hukumar Jibia, inda suka kashe mazauna garin hudu tare da jikkata wasu mutum shida.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe manyan ƴan bindiga 3 yayin musayar wuta a dajin iyakar Abuja da Kaduna

Wani mazaunin ƙauyen da ya tabbatar aukuwar lamarin ta wayar tarho, ya kuma ƙara da cewa maharan sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba, yawancinsu mata da yara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, bai bayar da amsar tambayar da aka yi masa ba kan lamarin.

Sai dai, da Legit Hausa ta tuntuɓi mataimakin ƴan sakai na ƙaramar hukumar Jibia, Malam Nasiru, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa a cikin ƴan kwanakin nan an samu hare-haren ƴan bindiga a yankin.

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sanye da kayan sojoji sun yi awon gaba da mutum 30 a wani sabon hari a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tashar Nagule a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng