Rikicin Plateau: Ahmed Musa Ya Yi Magana Mai Zafi Kan Matsalar da Ke Faruwa, Ya Tura Sako
- Fitaccen dan wasan kwallon kafa a Najeriya, Ahmed Musa ya bukaci a hada kai don dawo da zaman lafiya a Plateau
- Musa ya bukaci jama'a su hada kai tabbatar da zaman lafiya yayin da kashe-kashen ke wuce gona da iri
- Dan wasan ya bayyana haka a yau Alhamis 25 ga watan Janairu a shafinsa na X kan rikicin jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Yayin da rikicin jihar Plateau ke kara kamari, don wasan Najeriya, Ahmed Musa ya tura sako.
Musa ya bukaci jama'a su hada kai tabbatar da zaman lafiya yayin da kashe-kashen ke wuce gona da iri.
Mene Musa ke cewa kan rikicin Plateau?
Dan wasan ya bayyana haka ne a shafinsa na X yayin da ya ke tare da tawagar 'yan wasan Najeriya a gasar AFCON.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitaccen dan wasan ya bukaci 'yan siyasa su yi mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya kamar yadda aka yi a baya.
Ya ce:
"Ina rokon zaman lafiya a Plateau, ya ku 'yan uwa a Plateau da Najeriya baki daya.
"Ana cutar da Plateau, ya kamata mu hada kai, kashe-kashen ya yi yawa, mu 'yan uwa ne duk da bambancin addini.
"Mafi yawan iyalai a Plateau su na da 'yan uwa Musulmai da da Kirista, kamata ya yi mu yi murnar bambancinmu ba wai fada ba."
Shawarin Musa ga 'yan siyasa
Musa ya ce idan har muka hada karfi da karfe zamu yi nasara da yin addu'a ba tare da bambanci ba.
Musa ya kara da cewa:
"Ya kamata 'yan siyasa su ba da karfi wurin kare mu da dawo da zaman lafiya kamar yadda muka mora a baya.
"An san jihar Plateau a matsayin jihar zaman lafiya da yawon bude ido, muna bukatar hakan a yanzu ma."
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin addini da kabilanci ke kara kamari a karamar hukumar Mangu da ke jihar, cewar Leadership.
Rundunar tsaro ta yi martani kan rikicin Plateau
Kun ji cewa, rundunar tsaro a Najeriya ta yi martani kan zargin hannu a rikicin kabilanci a jihar Plateau.
Rundunar ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo cewa su na kashe Kiristoci a rikicin da ya kara dagulewa.
Asali: Legit.ng