Jami'an Tsaro Na da Hannu a Kisan Kiyashin da Ke Wakana a Plateau? Gaskiya Ta Bayyana
- Rundunar tsaro a Najeriya ta yi martani kan zargin saka hannunta a rikicin kabilanci a jihar Plateau
- Rundunar ta karyata hakan inda ta ce babu kamshin gaskiya tattare da labarin wanda babu wata hujja
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani jami'in tsaro kan wannan rikicin kabilanci da ke faruwa a Plateau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rundunar tsaro Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa jami'an tsaro sun farmaki Kiristoci a jihar Plateau.
Rundunar ta karyata hakan inda ta ce babu kamshin gaskiya tattare da labarin wanda babu wata hujja.
Wane martani rundunar ta yi?
Rundunar ta bayyana haka ne a shafinta na X a yau Alhamis 25 ga watan Janairu kan wannan lamari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan martani na zuwa ne bayan shugaban kungiyar Kiristoci, CAN a jihar, Rabaran Timothy Daluk ya zargi jami'an tsaro da goyon bayan wani bangare a rikicin.
Rundunar ta ce kawai nema ake yi a bata sunan rundunar tsaron kasar da karairayi marasa tushe da asali cewar ta na kashe Kiristoci.
Wace shawara rundunar ta bayar?
Ta ce abin takaici ne yadda shugaban CAN da ake zaton koyar da zaman lafiya zai neman ta da zaune tsaye da bata sunan rundunar, cewar TheCable.
Ta bukaci al'umma da su yi watsi da wannan jita-jita inda ta ce har gobe jami'an tsaro ba sa goyon bayan ko wane bangare a rikicin.
Har ila yau, rundunar ta godewa jama'a musamman wadanda su ke bin doka a yankunan tare da ba su goyon baya a kokarin tabbatar da zaman lafiya.
Sanarwar ta ce:
"Mun samu labarin wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar CAN a jihar, Rabaran Timothy Daluk ke neman bata sunan rundunar soji.
"Babu kamshin gaskiya a bidiyon da ke zargin jami'an tsaro su na goyon bayan wani bangare a rikicin.
"Abin takaici ne haka ya fito daga shugaban addini da ake tsammani koyar da zaman lafiya, rundunar ba ta goyon bayan ko wane bangare a kokarin tabbatar da zaman lafiya."
Legit Hausa ta ji ta bakin wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa kan lamarin.
Sojan ya ce wannan zargi da ake yi ba zai taba faruwa ba saboda a tsarin aikin babu gurbin haka.
Ya ce:
"Mu a tsarin aikinmu an koya mana gudanar da aiki ba tare da nuna wani bangaranci na addinin ko kabila ba."
Ya ce sai dai idan wasu ne ke shigar sojoji kamar yadda wasu 'yan bindiga ke yi yayin hare-harensu.
Ana zargin jami'an tsaro da hannu a rikicin Plateau
Kun ji cewa jama'a da dama na zargin jami'an tsaro da hannu a rikicin da ake fama da shi a jihar Plateau.
Al'ummar da ke zaune a karamar hukumar Mangu sun zargi jami'an tsaron 'Operation Rainbow' da aikata laifukan kisan kai da kona gidaje.
Asali: Legit.ng