Yadda Gwamna Ya Bar Aikin Gabansa, Ya Shilla Kasar Waje Aka Cashe na Kwanaki
- An yi kwana da kwanaki Mai girma Babajide Sanwo-Olu bai Legas, ya tafi biki a wara kasar ketare
- Ana zargin gwamnan jihar Legas yana cikin wadanda suka halarci bikin Aisha Achimugu @ 50
- Miliyoyi sun yi ciwo a wannan biki da aka yi a tsibirin Grenada domin taya ‘yar kasuwar murna
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Lagos - A ranar Laraba ake zargin Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya dawo Najeriya daga tsibirin Grenada inda ya halarci biki.
A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an ce gwamnan na jihar Legas ya halarci bikin da Aisha Achimugu ta shirya.
Aisha Achimugu tayi biki a kasar ketaren inda manyan mutane suka cashe domin taya ‘yar kasuwar murnar cika shekaru 50.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sanwo Olu ya kashe $130, 000 a otel
Babajide Sanwo-Olu wanda ya zarce a 2023 ya dauki hayar jirgin yawo daga Najeriya zuwa tsibirin, kuma ya zauna a katafaren otel.
Rahoton yace otel din da gwamnan ya tare yana cikin mafi tsada a duniya, daga baya ya nuna aiki ya kai shi waje ba shakatawa ba.
Bincike ya sa an gano cewa a dakin da gwamna Sanwo Olu ya rika kwana a tsibirin Calivigny, ana biyan $132,000 a kowane dare.
Sanwo-Olu da sauran wadanda suka je wannan biki sun rika kwana ne a Calivigny Island da wani otel mai suna Silversand Grenada.
A tsawon kwanaki bakwai, ana tunanin an yi bindiga da $924,000 a kan wurin kwana ban da sauran kashe-kashen kudi da aka yi.
Gwamna ya je bikin Aisha Achimugu @50
An fara gagarumin bikin da Aisha Achimugu ta shirya ne da liyafar kumallo a ranar 17 ga Junairu, haka aka yi gwangwaje har dare.
Jaridar tace Sanwo Olu bai iya zuwa ba sai bayan kwanaki biyu, a nan ya zauna har zuwa Talata, haka ya bar ofishinsa a Ikeja wayam.
Ina Gwamnan Legas ya shiga?
Jami’an gwamnatin jihar Legas sun yi kwana da kwanaki ba su san inda Babajide Sanwo-Olu ya shiga ba, an boye masu lamarin.
An sanar da wasu cewa aikin ofis ya kai gwamnan birnin Landan, wasu jami’an kuma sun tafi a kan ya tafi wasu harkoki ne a waje.
Hotunan da gwamnan ya fitar a X sun nuna ya hadu da Firayim Ministan Grenada, Dickon Mitchell, domin a kawowa Legas cigaba.
Ba a tabbatar da alakar gwamna da Achimugu ba, ko ya abin yake dai an shakata da wasannin Waje, Flavour, Adekunle Gold da Asake.
Asali: Legit.ng