Rai bakon duniya: Yadda wata Kada ta yi kalaci da wata Uwa da jariryarta

Rai bakon duniya: Yadda wata Kada ta yi kalaci da wata Uwa da jariryarta

Kaico, ba mutuwa ake tsoro ba, hanyoyin mutuwar ake ji, don kuwa idan ajali yayi kira tabbas ko ba ciwo sai an je, hakan ne ya tabbata akan wasu masoya biyu, Uwa da diyarta, inda suka gamu da mummunan ajali a kasar Uganda.

Wata mata da diyarta sun fuskanci mutuwarsu a hannnun wani mayuwacin Kada a ranar Juma’ar data gabata a kasar Uganda, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya ya bayyana.

KU KARANTA: Buhari ya fidda dala biliyan 1 don gudanar da wasu muhimman ayyuka 3 a kudu 2 a Arewa

Rai bakon duniya: Yadda wata Kada ta yi kalaci da wata Uwa da jariryarta
Wani Kada
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a tafkin Albert dake yankin Arewa maso yammacin kasar Uganda, inda matar ta tafi debo ruwa dauke da jaririyarta yar watanni biyar a bayanta.

Hukumar kula da namun daji ta kasa ta bayyana kisan a matsayin wani hari da namun daji ke kaiwa mutane, wanda ta bayyana cewa yana faruwa ne a lokacin da dabbobi ke gasar neman abinci a tsakaninsu, sa’annansu kuma jama’an yankin basu da ruwan famfo, don haka suke fita neman ruwa.

“Muna shawartar jama’a dasu guji duk wani yankin da ake samun Kadoji masu cin naman mutum, su Kadoji suna zama ne a inda ake samun kifaye a cikin rafi ko tafki, amma idan adadin kifayen dake ruwan suka ragu, sai su fito waje suna su yi farautar mutane.” Inji kaakain hukumar, Bashir Hangi.

Rahotanni sun tabbatar da cewar mazauna yankin da wannan mummunan hadari ya faru sun yi iya bakin kokarinsu don ceto matar da jaririyartata, amma basu samun nasara ba, yayin da tuni Kadar yayi awon gaba dasu cikin ruwa.

A wani labarin kuma, wani jami’in hukumar kare namun daji na kasar Uganda yace ana iya kama Kadar daga baya, inda yace a ko a ranar Asabar din data gabata sai da suka kama wani Kada mai tsawon kilomita 700 daya cinye mutane biyu a shekarar 2013.

“A yanzu haka ina yankin tsakiyar Uganda, Ngoma, inda farautar wani Kada daya cinye bunsurai guda 32 a wani kauye, don haka muna kamasu.” Inji jami’i Peter Ogwang.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel