Buhari Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ya Ki Fito Da Sakamakon WAEC Dinsa a 2015
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce da gangan ya ki fitar da sakamakon WAEC dinsa a lokacin da aka matsa masa a 2015
- A cewar Buhari, yana tare da sakamakon jarrabawar tun a shekarar 2018 amma ya ki fitar da shi don ba 'yan adawa damar yin kumfar baki
- Femi Adesina, tsohon mai ba Buhari shawara ta fuskar watsa labarai ya bayyana hakan littafin da ya wallafa na rayuwar shugabancin Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Da gangan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki bayyana sakamakon jarabawarsa ta WAEC duk da matsin lambar da ya sha a zagaye zaben 2015.
A cewar Buhari, tun a shekarar 2018 ya ke tare da sakamakon jarabawar amma yaki bayyana shi don ba 'yan adawa damar ci gaba da kumfar baki akan takardar.
Buhari ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina cikin duba kayana na ci karo da takardar kammala makarantar sakandare, amma da gangan naki fitar da shi a fili".
Femi Adesina ya yi bayani game da karatun Buhari
Daily Trust ta ruwaito tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan a sashe na 5 na littafin da tsohon hadiminsa ta fuskar watsa labarai, Femi Adesina ya wallafa.
Littafin mai taken: Aiki da Buhari - Mahangar mashawarcin shugaban kasa ta fuskar watsa labarai (2015-2023), an kaddamar da shi a Abuja, wanda ya yi bayani kan shugabancin Buhari.
A iya tunawa cewa a watan Nuwamba 2018, magatakardar hukumar WAEC da wasu jami'an hukumar suka kai wa shugaban kasar takardar shaidar kammala karatunsa na sakandare, The Cable ta ruwaito.
Adesina ya ruwaito Buhari na cewa:
"Da ace ban zana jarrabawar WAEC a 1961 ba, da ba zan samu damar zuwa kwalejin tsaro a India (1973) ko kwalejin sojoji ta Amurka ba, kasancewa ta jami'in sojan Najeriya."
A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa
Buhari, Yar'Adua sun yanke shawar shiga aikin soja
Ya tariyo irin yadda rayuwa take a zamanin su, inda ya ce abu ne mai wahalar gaske mutum ya aikata laifin satar jarrabawa, duk da cewa ba wai za a iya gaza yin hakan ba.
Buhari ya ce:
"Ni da abokan karatuna da muka shafe shekaru 9 a makarantar kwana a firamare da sakandire, da suka hada da Janar Musa Yar'Adua, mun yanke shawarar shiga aikin soja tun a lokacin.
"Mun zana jarabawa a darussa uku, Turanci, Lissafi da Ilimin bai daya saboda Turanci shi ne yaren bai daya a kasar bayan zama karkashin turawan mulkin mallaka."
Dabarun horon soja a zamanin su Buhari
Game da yadda horo ya kasance na shiga aikin soja, tsohon shugaban kasar ya ce:
"Dole ne sai ka iya lissafi kafin shiga aikin soja, sannan ka haɗa da ilimin sanin taswirar kasa. An horas da mu yadda za mu shiga jejiz mu yi amfani da kamfas don neman hanya.
"Mukan yi amfani da dabarar Pythagoras Theorem da wasu dabarun da muka koya a makaranta don sanin inda muke da inda za mu dosa a cikin jejin."
Kisan Ummita: Kotu za ta yanke wa dan China hukunci
A wani labarin kuma, wata babbar kotu a Kano ta saka ranar 29 ga watan Maris don yanke hukuncin karshe kan dan China da ake zargin ya kashe 'yar Najeriya.
A watan Satumba 2022 ne aka yi zargin Mr Geng ya kashe budurwarsa Ummukulsum a gidansu da ke Jambulo Quarters, Kano.
Asali: Legit.ng