Hukumar Jarabawar WAEC ta bayyana rashin bayyanar darussa biyu a Takardun Shugaba Buhari

Hukumar Jarabawar WAEC ta bayyana rashin bayyanar darussa biyu a Takardun Shugaba Buhari

Hukumar jarabawar nan ta WAEC, ta yi karin haske tare da mayar da martani dangane da sabanin sakamakon shaidar takardun shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gabatar a shekarar 2015 da kuma wanda ta gabatar a jiya Juma'a 2 ga watan Nuwamba na shekarar 2018.

Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporter ya ruwaito, an samu sabani na raguwar adadin darussa da suka bayyana cikin sakamakon shaidar shugaba Buhari da aka gabatar a shekarar 2018 da kuma wanda hukumar ta gabatar a shekarar 2015 da ta gabata.

Hukumar Jarabawar WAEC ta bayyana rashin bayyanar darussa biyu a Takardun Shugaba Buhari
Hukumar Jarabawar WAEC ta bayyana rashin bayyanar darussa biyu a Takardun Shugaba Buhari
Asali: Twitter

A sanadiyar haka hukumar ta bayyana cewa, a halin yanzu ta dauki wani sabon salo na rashin bayyana darussan da ba a samu nasara ba yayin zaman zana jarabawar, inda ta dauke darasin lissafi watau Mathematics da kuma darasin Wood Work wanda shugaba Buhari bai samu nasararsu ba.

Darussan biyu sun yi layar zana cikin takarda ta shaidar sakamakon shugaba Buhari, sabanin darussan English Language, Literature-in-English, Hausa Language, History, Geography, Mathematics, Health Science da kuma Wood Work da suka bayyana cikin sakamakon da hukumar ta gabatar a shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Okorocha da Amosun abin kunya ne ga jam'iyyar APC - Oshiomhole

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta WAEC ta yi wannan karin haske cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na zauren sada zumunta da ta bayyana cewa, ba bu wani darasi da zai sake bayyana cikin takardarta ta shaida matukar ba a yi nasararsa ba yayin gudanar da zama na zana jarabarwar.

Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, a yau Asabar kungiyar 'yan kasuwar kabilar Ibo ta ziyarci shugaban kasa Buhari a fadarsa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel