Sakataren Harkokin Kasar Amurka Ya Sa Labule da Tinubu Bayan Ya Iso Najeriya, Bayanai Sun Fito

Sakataren Harkokin Kasar Amurka Ya Sa Labule da Tinubu Bayan Ya Iso Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Antony Blinken sakataren harkokin ƙasar Amurka ya iso Najeriya inda zai gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa
  • An tattaro cewa sakataren harkokin ƙasar Amurka ya sauka ƙasar ne da misalin ƙarfe 4:40 na yamma, bayan ya ƙara mintuna 35 kan lokacin da aka shirya zai iso
  • Blinken ya samu tarba daga George Akume, sakataren gwamnatin tarayya da Yusuf Tuggar, ministan harkokin wajen Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sakataren harkokin ƙasar Amurka, Antony Blinken, ya iso Najeriya domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa.

Rahotanni sun ce Blinken ya iso Najeriya ne da misalin ƙarfe 4:40 na yamma, mintuna 35 bayan lokacin da aka yi tsammanin isowarsa.

Kara karanta wannan

Ana cikin rade-radin dawowar Ƙwankwaso APC, Ganduje ya sha sabon alwashi kan abu 1

Anthony Blinken ya iso Najeriya
Anthony Blinken ya iso Najeriya don ganawa da Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, US Secretary of State Antony Blinken
Asali: Twitter

Tashar talabijin ta TVC ta ruwaito cewa sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da ministan harkokin ƙasashen waje, Yusuf Tuggar ne suka tarbe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa saboda zuwan da ya yi a makare, kai tsaye ayarin nasa suka nufi fadar Villa domin halartar ganawar da zai yi da Shugaba Tinubu da ƙarfe 6:00 na yamma

Antony Blinken zai yi magana da manema labarai nan take bayan ya gana da shugaban ƙasar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Yaushe Blinken Zai Bar Najeriya?

Da misalin ƙarfe 10 na dare zai bar Abuja zuwa Legas domin ganawa da ƴan kasuwa da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu kafin ya tafi Angola a ranar Laraba 24 ga watan Janairu.

Gobe ​​da daddare zai tashi zuwa Angola. Najeriya ita ce ƙasa ta uku da ya kai ziyara a ziyarar da yake yi a nahiyar Afirika domin ƙulla kyakkyawar alaƙa da hadin gwiwa tsakanin Amurka da nahiyar Afirika.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar dokoki ya aike da saƙo na musamman kan nasarar gwamnan arewa a Kotun Ƙoli

Tinubu Ya Gana da Shugabannin Ƙungiyar CAN

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya labule da shugabannin ƙungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN), a fadarsa da ke Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.

Ganawar dai na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan majalisar ƙoli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta gana da Tinubu a Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel