An Kama Wani Matashi, Yusuf, a Hanyarsa Na Zuwa Kai Wa ’Yan Ta’adda Harsashi a Dajin Zamfara

An Kama Wani Matashi, Yusuf, a Hanyarsa Na Zuwa Kai Wa ’Yan Ta’adda Harsashi a Dajin Zamfara

  • Rundunar 'yan sanda ta kama Mansir Hassan, wanda ke yi wa 'yan ta'adda safarar makamai a dajin Zurmi, jihar Zamfara
  • Jami'an rundunar na ofishin Tudun Wada Zariya a jihar Kaduna ne suka kama Yusuf dauke da daruruwan harsasai a hanyar zuwa Zamfara
  • An gano cewa Yasuf ya karbi harsasan a karamar hukumar Kauru, inda zai kai wa wani dan bindiga mai suna 'Emir' a dajin Zurmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wani mai siyar da bindigogi wanda ke kai wa 'yan ta'adda makamai a dajin Zamfara.

A wata sanarwa a ranar Talata, Mansir Hassan, kakakin rundunar a Kaduna ya ce mutumin mai suna Musa Yusuf ya shiga hannu a hanyarsa ta zuwa Zamfara kan babur.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugabanta, ta fadi babban dalili 1

An kama mai kai wa 'yan bindiga harsashi a Zamfara
Kaduna: An kama wani matashi da jakar harsasai zai kai wa 'yan bindiga a Zamfara. Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

An gano wanda Yusuf zai kaiwa harsasai a dajin Zurmi

Kakakin rundunar ya ce Yusuf ya karbi harsasai a Bakin Kogi da ke karamar hukumar Kauru da ke jihar, kamar yadda The Cable ya ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf ya ce:

"Binciken farko ya tabbatar da cewa Musa Yusuf ya karbi harsasai a Bakin Kogi a karamar hukumar Kauru, jihar Kaduna inda zai kai wa wani dan bindiga mai suna 'Emir' a dajin Zurmi.

Jami'an 'yan sanda na ofishin rundunar da ke Tudun Wada Zariya sun kama shi ne bayan karbar harsasan, yana hanyar zuwa kai wa dan bindigar a Zamfara."

Ana shirin kama masu taimakawa Yusuf wajen safarar makamai

Ya ce wanda aka kaman ya ranta a na kare da ya hango jami'an tsaron, inda ya bar babur da jakar da ya dauko wacce ke dauke da harsasai 202 masu tsayin mita 7.62 x 39.

Kara karanta wannan

Kano: Tashin hankali yayin da matashi ya sheke abokin aikinsa a Kamfani, matasa sun tafka barna

Leadership ta ruwaito Mr Hassan ya kuma jinjinawa jami'an rundunar da suka bi bayan Yusuf har suka kama shi tare da tatsar wasu bayanan sirri daga wajen sa.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa bincike ya yi nisa na yadda za a kama wadanda ke taimakawa Yusuf a safarar makaman.

Mata da miji sun yi garkuwa da kansu don neman kudi

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Legas sun kama wata mata da mijinta da suka yi garkuwa da kansu tare da neman naira miliyan biyar daga 'yan uwansu matsayin kudin fansa.

Rundunar ta kuma kama wasu mutanen a Abuja da Filato wadanda suka kware a yin garkuwa da kansu duk don neman kudi daga 'yan uwansu, wanda rundunar ta ce hakan laifin ne babba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.