‘Yan sanda sun damke kasurgumin mai siyar da makamai ga ‘yan fashi a Katsina

‘Yan sanda sun damke kasurgumin mai siyar da makamai ga ‘yan fashi a Katsina

  • ‘Yan sandan Najeriya sun kama Ibrahim Abdullahi mai shekaru 40 a Katsina
  • Ana zargin cewa Abdullahi mai siyar da makamai ne ga ‘yan bindiga a sassa daban-daban na kasar
  • An kuma kama shi ne tare da ‘yan kungiyarsa su hudu da kuma kudade da bindiga

‘Yan sanda a Katsina a ranar Juma’a, sun gurfanar da wani fitaccen mai sayar da makamai ga ‘yan fashi, Ibrahim Abdullahi mai shekaru 40.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya kware sosai wajen samar da bindigogi zuwa sansanonin ‘yan fashi a sassa daban-daban na kasar, an kuma kama shi ne tare da ‘yan kungiyarsa su hudu.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna

‘Yan sanda sun damke kasurgumin mai siyar da makamai ga ‘yan fashi a Katsina
‘Yan sanda sun kama Ibrahim Abdullahi mai siyar da makamai ga ‘yan fashi a Katsina Hoto: The Nation
Asali: UGC

Hakanan, an kwato kudi N3, 445, 000: 00 da bindiga 1 AK-47 daga hannun wadanda ake zargin, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

A yayin da yake sanarwa manema labarai nasarorin da rundunar ta samu a kwanan nan a yayin yaki da 'yan ta'adda da sauran masu laifuffuka a Katsina a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina, SP Gambo Isah, ya ce a lokacin da suke amsa tambayoyi, shugaban kungiyar, ya amsa cewa shi mai siyar da bindigogi ne.

Ya kuma bayyana cewa sun dauki bindigogi kirar AK-47 guda shida zuwa ga wani sanannen shugaban 'yan fashi da ake kira: Tukur Rabiu, wanda aka fi sani da "Nasharme" a dajin Rijana, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma sun amshi kudin.

Ya ce:

“Wata tawaga ta jami’an yan sanda masu sintiri, da ke sintiri akan hanyar Tsaskiya - Ummadau, karamar hukumar Safana ta jihar Katsina ne suka tare Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 40, Tukur Musa, mai shekaru 35, Abubakar Ibrahim, mai shekaru 21 da Rabi’u Hamisu, mai shekaru 19 akan babura da ake zargin mallakar 'yan fashi ne. A yayin gudanar da bincike, shugaban tawagar ya furta cewa ana biyan shi kudi N100,00 a kan kowane bindiga.”

Mai magana da yawun rundunar ya kuma bayyana wani kame da aka yi yayin fashin barayi inda ‘yan bindigar da ke kan babura, suna harbi kan bindiga da bindiga kirar AK-47, suka far wa kauyen Tinya, da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina kuma suka yi awon gaba da wasu dabbobi.

Ya ce:

“Tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wata kungiyar ‘yan banga sun fatattaki ‘yan bindigar, inda suka yi musayar wuta da su, suka kashe daya daga cikin ‘yan fashin, sannan suka kwato bindiga AK-47 guda daya. Nan da nan jami'an tsaro suka duba lamarin inda suka samu nasarar kwato shanu 12 da tumaki 11, wadanda barayin suka sace.”

Sojoji sun cafke yaron Jagoran ‘Yan Boko Haram a Borno, ya yi maza ya hadiye layin SIM a baki

A wani labarin, dakarun sojin Najeriya sun cafke wani matashi mai suna Wida Kachalla, wanda ake zargin yaron Modu Solum ne.

Shi wannan Modu Solum ya na cikin jagororin sojojin kungiyar Islamic State in West Africa Province da su ka dade suna addabar Arewa maso gabas.

Rahoton ya ce Wida Kachalla mutumin garin Murguba ne a jihar Borno. An ce wannan kauye ya yi kaurin suna wajen tara ‘yan ta’addan Boko Haram a yanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel