Kwankwaso Butulu Ne: Yanzu Muka Fara Adawa da Gwamnatin Kano, In Ji Dan Bilki Kwamanda

Kwankwaso Butulu Ne: Yanzu Muka Fara Adawa da Gwamnatin Kano, In Ji Dan Bilki Kwamanda

  • Mai fashin baki a harkokin siyasar jihar Kano kuma sojan baka, Dan Bilki Kwamanda, ya caccaki jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso
  • A cewar Dan Bilki Kwamanda, yanzu ne suka fara yin adawa da gwamnatin Kano, kuma sai sun binne siyasar Kwankwso
  • Legit Hausa ta zanta da Sarkin Tafiya daga Dawakin Tofa wanda ya ce bai kamata ana barin irin su Kwamanda suna zama cikin mutane ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Wani sojan baka a siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da dadewa ba za su kawo karshen siyasar jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwamanda ya ce yayi mamakin yadda har Tinubu ya tsorata da Kwankwaso, wanda a cewar sa shi Kwankwaso 'duba gari ne' wanda bai kamata aji tsoron sa ba.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya yi magana kan yiwuwar Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC su sake haɗuwa

Dan Bilki Kwamanda ya yi wa Kwankwaso kaca-kaca
Kwankwaso matsoraci ne, mun kusa binne siyasarsa a Kano - Dan Bilki Kwamanda. Hoto: @KwankwasoRM, @kokikano3
Asali: Twitter

Legit Hausa ta ci karo da tattaunawar da aka yi da mai fashin baki kan harkokin siyasar jihar, a wani bidiyo da aka wallafa a shafin @danbalkicommander a TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamanda ya ce yanzu suka fara adawa da Kwankwaso

A cikin bidiyon, wanda kuma wani Enjiniya Alkassim Fge ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ji Dan Bilki Kwamanda na cewa:

"Yanzu muka fara adawa da gwamnatin Kano, kuma babu wanda ya isa ya hana mu kalubalance su tun daga kan shi wannan Rabiu Kwankwason.
"Ai Rabiu Kwankwaso butulu ne a siyasa, har na yi mamakin yadda aka tsorata Bola Tinubu da Kwankwaso. Matsoraci ne a siyasa mara kunya."

Akwai mutane masu mutunci a jam'iyyar NNPP - Kwamanda

Mai fashin bakin ya kuma ce yanzu ne Rabiu Kwankwaso zai fara ganin adawa a wajen su, kuma ba sa shakkar kowa a jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya nemi korar mutum 3 a APC, a dauko Kwankwaso daga NNPP

Sai dai ya ce akwai mutanen kirki a jam'iyyar, wadanda suke biyayya don karbo dukiyarsu da suka kashe, ba wai don suna son jagoran jam'iyyar ba.

Ya yi ikirarin cewa:

"Idan kana neman butulu a siyasa ka hadu da Rabiu Kwankwaso to magana ta kare, don haka babu abin burgewa a yi alfahari da dan siyasa irinsa."

Kalli bidiyon a kasa:

Jami'an tsaro sun kyauta da suka kama Dan Bilki Kwamanda

Da ya ke tsokaci kan furucin Dan Bilki Kwamanda, wani Isma'il Sarkin Tafiya, a Dawakin Tofa da ke jihar Kano, ya ce bai kamata a bar ire-iren Kwamandan suna yawo a gari ba.

A zantawarsa da Legit Hausa, Sarkin Tafiya ya ce:

"Ire-iren su Dan Bilki Kwamanda barazana ne ga zaman lafiyar al'umma, babu komai a furucinsa face karya da cin mutuncin mutane.
"Yanzu da ya ci wa Kwankwaso mutunci, idan magoya bayan jagoran suka ce za su dauki doka a hannun su, me kake tunanin zai faru?"

Kara karanta wannan

"Ba zai illata arewa ba": Jigon PDP ya magantu kan mayar da manyan ofisoshi Legas

Sarkin Tafiya ya ce ya ji dadi da aka ce jami'an tsaro sun kama Kwamanda har an kai shi 'gidan dan kande'.

"Yanzu da aka garkame shi wa gari ya waya? Ai na ji dadi sosai da aka kama shi, hakan zai zama izina ga duk masu son cin mutuncin mutane masu daraja da sunan siyasa."

A cewar Sarkin Tafiya.

Kwankwaso ya jinjinawa tawagar Najeriya a gasar AFCON

A wani labarin, jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso ya jinjinawa kokarin tawagar Najeriya ta Super Eagles bayan lallasa Guinea-Bissau a gasar kofin Nahiyar Afirka.

A jiya Litinin ne Super Eagles suka kara da Guinea-Bissau inda wasan ya tashi 1-0, wanda ya ba Najeriya damar zuwa mataki na gaba tare da sallamar Guinea-Bissau daga gasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.