Yan Sanda Sun Kama Makanike Da Ya Tsere Da Motar Kwastoma Bayan Kawo Masa Gyara a Legas

Yan Sanda Sun Kama Makanike Da Ya Tsere Da Motar Kwastoma Bayan Kawo Masa Gyara a Legas

  • Rundunar 'yan sanda sun kama wani makanike da ya sace motar wani kwastomansa a yankin Isheri-Oshun da ke jihar Legas
  • Makaniken mai shekaru 54, ya fakaici lokacin da kwastoman nasa ya tafi coci, ya je gidansa ya karbi makullin motar tare da gudawa da ita
  • Rundunar ta kuma kama wani Charles Nnoli mai shekaru 47 wanda makaniken ya kaiwa motar kirar Nissan Xterra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - An kama wani makanike mai shekaru 54 mai suna Abisodun Ilori da laifin satar mota a yankin Isheri-Oshun na jihar Legas.

Punch Online ta gano cewa kama Ilori ya biyo bayan korafin da wani mazaunin yankin ya yi game da bacewar motarsa kirar Nissan Xterra.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wata mata ta jefa jaririnta cikin kogi, yan sanda sun dauki mataki

An kama barawon mota a Legas
Yan sanda sun kama makanike da ya sace motar kwastoma a Legas. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

An tattaro cewa mai motar ya tafi coci ne a ranar Lahadi lokacin da Ilori ya ziyarci gidansa, inda ya karbi makullan motar daga hannun ‘yarsa, ya gudu da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wanda makaniken ya kaiwa motar bayan satar ta

Wata majiya ta ‘yan sanda ta shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa, DPO mai kula da yankin ya ba jami’an yaki da satar mota umurnin bin diddigin lamarin satar motar.

Ya ce:

"Daga baya an kama wanda ake zargin ta hanyar tattara bayanan sirri kuma ya jagoranci jami'an zuwa ga Charles Nnoli mai shekaru 47 wanda ya sayi motar daga gare shi."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kuma kama mai sayen motar tare da kwato motar.

Kara karanta wannan

Ana kukan ba kudi, Wike zai gina katafariyar makarantar sakandare a Abuja, za ta lakume N1.7bn

Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ana fargabar zabtarewar kasa ta halaka leburori uku a Nasarawa

A wani labarin kuma, a safiyar yau Litinin aka tashi da wani mummunan labari a jihar Nasarawa bayan da kasa ta rufta kan wasu leburori da aikin hakar kasar.

An ruwaito cewa lebura daya ya kubuta amma har yanzu ba a gano leburori uku ba, wadanda ake fargabar sun mutu la'akari da tsawon lokacin da suka dauka a karkashin kasar.

Tuni dai jami'an ceto da al'ummar garin ke ci gaba da tono kasar da zummar nemo gawarwakin leburorin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel