“An Yi Masa Mugun Duka”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Shugaban Makarantar Kaduna Ya Shaki Yanci

“An Yi Masa Mugun Duka”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Shugaban Makarantar Kaduna Ya Shaki Yanci

  • Shugaban makaranta da yan bindiga suka tsare bayan ya kai masu kudin fansa a madadin wadanda aka sace ya shaki iskar yanci
  • Sanata Shehu Sani ya tabbatar da ci gaban a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a rsafiyar anar Talata
  • Ya bayyana cewa shugaban makarantar ya shaki yanci bayan yan bindigar sun yi masa mugun duka da kuma biyan kudin fansarsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sako Mallam Abdulkadir, shugaban makaranta mai ritaya a Kaduna wanda aka tsare yayin da ya je kai kudin fansa a jihar Kaduna.

Mallam Abdulkadir ya shaki isakar yanci bayan yan bindiga sun tsare shi
“An Yi Masa Mugun Duka”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Shugaban Makarantar Kaduna Ya Shaki Yanci Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ne ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na X, a ranar Talata, 23 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

"A nemo mun ita: Bidiyon wata yar makaranta tana Sallah a kan hanya ya dauka hankalin jama'a

Tsohon dan majalisar na PDP ya bayyana cewa Mista Abdulkadir ya biya kudin fansar sakinsa amma sai da yan bindigar suka yi masa mugun duka saboda jinkiri da aka samu wajen biyan kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya rubuta:

"An sako Mallam Abdulkadir, shugaban makarantar Kaduna mai ritaya wanda masu garkuwa da mutane suka tsare shi wajen kai kudin fansa a safiyar yau.
"An biya kudin fansar sakinsa. An yi masa mugun duka kuma ya rasa hakorinsa saboda jinkiri wajen biyan kudin."

Jama'a sun yi martani

Halin da shugaban makarantar ya shiga ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu a dandalin X. Legit Hausa ta tattare wasu daga cikin martanin a kasa:

@FirstObidient ya ce:

"Don Allah! Idan har sai sun biya kudin fansa, su nemi mutane irin su gumi ko irinsu waspapin. Kada a jefa rayuka masu amfani a hatsari."

Kara karanta wannan

"Taku ta ƙare" An kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi mutanen Abuja

@Chinonxo ta rubuta:

"Nan gaba kada ka taimaki kowa."

@mary_dozie ta ce:

"An gode Allah ya rayu."

@YakubuJonah5 ya ce:

"An gode Allah da rayuwarsa. Mutanen nan ba za su taba sanin kwanciyar hankali ba."

Yan bindiga sun kashe malamin makaranta a Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan bindiga sun kashe wani Mallam Idris Abu Sufyan, shugaban makarantar sakandare (GSS) Kuriga, karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe malamin ne a ranar Juma'a a lokacin da suka yi kokarin sace shi amma ya ki yarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng