Tsohon Janar Ya Saki Wasu Bayanai a Kan Hadarin Jirgin da Ya Kashe Hafsun Sojoji a 2021
- Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya yana zargin akwai ta-cewa a kan hadarin jirgin hafsun sojoji a 2021
- Sojan yace ba a ji labarin hakikanin abin da ya kashe Laftanan Janar Ibrahim Attahiru da tawagarsa ba
- A wata zantawa da aka yi da tsohon sojan, ya shaida yadda aka yi masa ritayar karfi da yaji a gidan soja
Abuja - Danjuma Ali-Keffi ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bincike a kan mutuwar Ibrahim Attahiru a jirgin sama.
Tashar RFI tace Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya ya gabatar da korafi bisa zargin tsare sa da yi masa ritaya ba tare da ka’ida ba.
Tsohon sojan yayi ikirarin an kore shi daga aiki ne saboda kokarin bankado jami’an gwamnati da ke daurewa ‘yan ta’adda gindi.
Mutuwar Janar Ibrahim Attahiru ta bar kura
Bayanan Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya sun fito a hirar da This Day tayi da shi a game da mutuwar hafsun da sojoji 11 a 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sojan ya rike GOC lokacin da Marigayi Laftanan Janar Ibrahim Attahiru yake ofis, ya ce ba a fito da binciken mutuwarsa ba.
Hadarin jirgin da walakin inji Janar Keffi
Ali-Keffi yace shi ya kamata ya tarbi Marigayin kafin jirginsa ya yi hadari, yana ganin akwai alamar tambaya kan abin da ya faru.
Janar din yace kwatsam aka canza lokacin tafiya, aka sauya wurin saukarsa daga filin saukar jiragen sojoji zuwa babban tashar jirgi.
Sojan yake cewa ya tuntubi abokan aikinsu da ya ji an canza lokacin tafiyar hafsun ganin cewa ana tsawa da sheka ruwan sama a ranar.
Tsohon sojan yana zargin mai gidansa da sauran jami’an sun babbake ne kafin a iya ciro gawarsu, babu rahoton binciken mutuwarsu.
Baya ga haka, tsohon GOC din yace an bata lokaci wajen tafiyar da sunan za a sauya jirgi, wannan duk ya jawo karin alamar tambaya.
Janar Attahiru ya so karya 'yan ta'adda
A cewar tsohon babban jami’in, mai gidansa ya yi kokarin kawo karshen ta’addancin da ake yi a Arewa, ya toshe hanyar samun kudi.
Lokacin Keffi ne shugaban sashen OSW da ke ruguza yadda ‘yan ta’adda ke samun kudi, bayan nan aka yi masa ritayar dole daga aiki.
Ina Bayo Omoboriowo ya san Buhari?
Dazu ne aka ji labarin yadda Mista Bayo Omoboriowo ya samu mukami a fadar shugaban kasa babu dangin iya ko baba a Aso Villa.
Akwai lokacin da Omoboriowo bai da dakin kwana, yana tallar ruwa a Mushin, bayan shekaru sai ga shi yana aiki da shugaban kasa.
Asali: Legit.ng