Manyan Sojoji sun fara rige-rige a kan wanda zai gaji kujerar Shugaban hafsun sojan kasa

Manyan Sojoji sun fara rige-rige a kan wanda zai gaji kujerar Shugaban hafsun sojan kasa

- Ana maganar wanda zai zama sabon shugaban sojojin kasa a Najeriya

- Abubuwan da za suyi aiki sun hada da matsayi, sanin aikin jami’in soja

- Ta tabbata rade-radin nada Janar Danjuma Ali-Keffi ba gaskiya ba ne

An soma harin kujerar shugaban hafsun sojojin kasa a Najeriya, hakan na zuwa ne bayan mutuwar Laftanan-Janar Ibrahim Attahiru a ranar Juma’a.

Jaridar Daily Trust ta ce rade-radin da ke yawo na nada Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a matsayin sabon hafsun sojan kasan Najeriya, ba gaskiya ba ne.

Asali ma akwai manyan sojojin kasa fiye da 30 a gaban Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi a yanzu.

KU KARANTA: COAS: Sojoji 4 da ake ganin za su dare kujerar Marigayi Janar Attahiru

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta na cewa watakila Mai girma Muhammadu Buhari ya dauko sojan Ibo a matsayin sabon hafsun soja na kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi hakan ne domin rufe-bakin masu kukan cewa ba a tafiya da jami’an yankin Kudu maso gabas wajen bada mukamai.

Masana suna ganin akwai bukatar a nada sabon hafsun saboda yakin da ake yi, amma jami’an tsaro suna ganin ya yi wuri da yawa a lokacin da suke makoki.

Wani masani a kan sha’anin tsaro, Kabiru Adamu, ya yi magana da ‘yan jarida, ya ce zai yi kyau shugaban kasa ya zabo kwararren sojan da ya san kan aiki.

Kabiru Adamu yake cewa abin da ya fi dacewa shi ne ayi watsi da batun kabilanci a gefe, a nemo jami’in da yake gogewa, kuma ya yi nisa a gidan sojan kasa.

KU KARANTA: An dauko jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi

Manyan Sojoji sun fara rige-rige a kan wanda zai gaji kujerar Shugaban hafsun sojan kasa
Marigayi Janar Attahiru Hoto:@hqnigerianarmy
Asali: Twitter

Idan har shugaban kasa ya zakulo sabon hafsu daga kudu maso gabashin Najeriya, surutun da ake yi na cewa gwamnatin nan mai-ci ta ware Ibo, zai ragu.

Matsalolin tsaro uku ne suke fuskantar kasar nan a yau; ‘yan ta’addan da suke tada kafar baya, miyagun ‘yan bindiga da kuma masu rajin a barka Najeriya.

Wani mai magana a kan abin da ya shafi kasa, Malam Abdulhaleem Ishaq Ringim, ya ce da shi yake da wuka da nama, da Manjo-Janar Ben Ahanotu zai nada.

A cewarsa, Janar Ahanotu ne ya yi nasarar cafke shugaban Boko Haram na farko, Mohammed Yusufu a 2009, yanzu shi ne jami’in da ke shirya tsare-tsaren sojoji.

Ku na da labari cewa hadarin jirgin sama ne ya yi sanadiyyar mutuwar Laftana Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan jami'an sojojin kasa a makon jiya.

Babban sojan kasan ya cika ne kwanaki kadan da jin labarin mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda rikicin cikin-gida ya ci shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel