Kaduna: Ashiru, Dan Takarar PDP Ya Fadi Abin da Zai Yi Nan Gaba Bayan Shan Kasa a Kotun Koli

Kaduna: Ashiru, Dan Takarar PDP Ya Fadi Abin da Zai Yi Nan Gaba Bayan Shan Kasa a Kotun Koli

  • Isa Ashiru, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kaduna da aka yi, ya magantu a karon farko bayan shan kaye a Kotun Koli
  • An shiru ya ce shan kaye a Kotun Koli ba shi ne karshen siyasar sa ba, yana mai cewa ya karbi hukuncin da zuciya daya
  • Sai dai har a yanzu dan takarar jam'iyyar adawar na ganin cewa shi ne halastaccen gwamnan jihar saboda kurakuran da ya ce an yi a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kaduna da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023, Isa Ashiru, ya ce ba zai bar siyasa ba duk da shan kasa a Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Yan sanda sun kama mutum 5 a Kano, sun tada zaune tsaye

Ashiru ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Kaduna ranar Litinin, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke na tabbatar da zaben gwamna Uba Sani.

Dan takarar PDP a Kaduna ya magantu bayan shan kasa a kotu
"Ban hakura ba," in ji Ashiru, dan takarar gwamnan Kaduna da ya sha kasa a Kotu. Hoto: @IsaAshiruKudan
Asali: Facebook

Ya kuma yi wa gwamnan fatan alkairi wajen tafiyar da al’amuran jihar yana mai cewa, “zan ba da gudunmowa ta idan har ya nemi hakan.”, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli sun yi watsi da karar Ashiru

A ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023 ne Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna,

Jam’iyyar PDP da Ashiru sun kalubalanci sakamakon zaben gwamnan da aka yi, inda suka yi zargin cewa ba Uba ne ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.

Sun kara da cewa an tafka kura kurai a zaben zaben saboda zargin cin hanci da rashawa da rashin bin ka’idojin dokar zabe ta 2022.

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

Sai dai a ranar Juma’a Kotun Kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Mohammed Ashiru Isa suka shigar.

Matakin da Ashiru ya dauka bayan hukunhukuncin Kotun Koli

Dan takarar gwamnan na PDP ya ce ya dauki hukuncin Kotun Kolin da zuciya daya, yayin da ya dage kan cewa bai fadi zaben gwamna a 2023 ba a jihar ba.

Ashiru wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya taba tsayawa takarar gwamna a 2019 amma ya sha kaye.

Ashiru ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’unsu ga jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta shirya gudanarwa a ranar 3 ga Fabrairu, 2024.

Rashin tsaro: Ministan Abuja zai gurfana gaban Majalisar Dattijai

A wani labarin kuma, Majalisar Dattijai ta ce za ta nemi zama da Nyesom Wike, ministan FCT domin jin shirin da ya yi na kawo karshen matsalar tsaro a birnin tarayya Abuja.

A baya bayan nan dai an ga yadda masu garkuwa suka addabi garuruwan Abuja, inda suka nemi miliyoyin kudade daga hannun wadanda suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.