Da Gaske ’Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar BUK? ’Yan Sandan Kano Sun Yi Karin Haske

Da Gaske ’Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar BUK? ’Yan Sandan Kano Sun Yi Karin Haske

  • Rundunar 'yan sanda ta karyata rahotannin ake yadawa na cewar masu garkuwa sun shiga dakin kwanan dalibai a jami'ar BUK da ke Kano
  • Rundunar ta ce jita-jita ce kawai mutane suke yadawa, inda ta gano cewa dalibai mata biyu ne kawai suka ce sun ji karar harbin bindiga
  • Sai dai a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, rundunar ta ce za ta kara saka ido tare da tsaurara bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce rahoton sace mutane a dakin kwanan dalibai mata jami'ar BUK a ba gaskiya ba ne, labarin kanzon kurege ne.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin ci gaba da sanya ido kan lamarin, biyo bayan rahotannin harbe-harbe a yankin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutumin da ya kitsa garkuwa da kansa don damfarar yan uwansa a Abuja

Yan sandan Kano sun yi karin haske kan zargin sace daliban BUK
Ba a yi garkuwa da daliban jami'ar BUK ba, ‘yan sandan Kano sun yi karin haske. Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Abin da 'yan sandan Kano suka ce kan jita-jitar

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Rahotanni daga jami’an mu a sabon matsugunnin jami'ar BUK na nuni da cewa zargin da ake yi na masu garkuwa da mutane sun je dakin kwanan dalibai mata mata ba gaskiya ba ne.
"A cikin dukkan mutanen da ke cikin dakin kwanan daliban, da suka hada da jami’an tsaro, dalibai mata 2 ne kawai suka ce sun ji karar harbin bindiga."

Da wannan ne rundunar ta ce, "Ana ci gaba da sa ido kuma an fara bincike.”

Karanta sanarwar a kasa:

Karin bayani kan daliban jami'ar Al-Qalam da aka sace

A wani labarin, jami'ar Musulunci ta Al-Qalam da ke jihar Katsina ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace dalibanta mata guda biyu a hanyarsu ta zuwa Katsina daga jihar Niger.

Kara karanta wannan

Dama ta samu yayin da Rundunar soji ta fara daukar sabbin sojoji, ta fadi yadda za a cike

Hukumar gudanarwar jami'ar ta ce tana kan tattaunawa da iyayen daliban tare da bibiyar rahotannin jami'an tsaro don jin halin da daliban suke ciki.

Tsawon kwanaki daliban suke hannun 'yan bindiga ba tare da sun kira waya don bayyana buƙatar su ta kudin da za a biya su na fansa kafin su sako su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.