Karar harbe-harben bindiga: Jama'a na zaman dar-dar a Maiduguri

Karar harbe-harben bindiga: Jama'a na zaman dar-dar a Maiduguri

Mazauna wasu unguwanni da ke gefen birnin Maiduguri sun shiga halin dar-dar biyo bayan jin karrar harbe-harben bindiga, lamarin da ya tilasta jama'a; maza da mata, manya da yara gudu domin neman tsira.

Mazauna yankin titin Damboa da filin wasan Polo sun fara jin karar harbe-harben bindigar tun da misalin karfe 3:00 na rana.

Sun bayyana cewar basu tabbacin su waye ke harbe-harben bindigar, ko sojoji ne ke gwajin wasu sabbin makamai.

Haruna Kachalla, wani mamba a kungiyar sa kai ta 'civilian JTF', ya ce sojojin da aka jibge a hanyar wani Otal da ke kan hanyar zuwa Damboa suka yi harb-harben yayin da suke kan hanyar su ta zuwa karbar aiki a wurin dakarun soji da ke yankin Molai.

"Da farko mun dauka cewar sojojin na gwajin makamai ne, amma da sojojin yankin Molai suka fara harba bindigar, sai jama'a suka fara gudu domin neman mafaka," a cewar Kachalla..

Bukar Mala, wani mazaunin titin Damboa, ya ce sun gudu ne bayan harbin bindigar daga wurare daban-daban ya ki kare wa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya raaito cewar gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bisa rakiyar dakarun hukumomin tsaro da na sa kai ya garzaya zuwa yankin domin ganin abin da ya ke faru wa.

Gwamna Zulum ya shaida wa manema labarai cewar babu abin damu wa tare da bayyana cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da cewar an samu zaman lafiya adukkan sassan jihar Borno.

"Duk da har yanzu bamu da tabbacin abin da ya faru, amma mun tabbatar da cewar ba harin mayakan kungiyar Boko Haram ba ne," a cewar sa.

Ya shawarci mazauna jihar da su guji yada jita-jita da kan iya tayar da hankulan jama'a haka kurum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel