Na Kusa da Shi Ya Bayyana Halin Tausayi da Buhari Ya Shiga Lokacin Rashin Lafiya
- Femi Adesina ya kawo zancen rashin lafiyar da Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da yake Aso Villa
- Tsohon shugaban kasar ya yi dogon jinya, mai magana da bakinsa ya yi maganar a cikin sabon littafinsa
- Adesina ya ce rashin lafiyar shugaban Najeriyan ya jawo bai san halin da yake ciki ba da ya kwanta jinya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Femi Adesina yana cikin masu magana da yawun Muhammadu Buhari, ya bada labari game da rashin lafiyar mai gidansa.
A littafin da ya rubuta a game da labarin gwamnatin Muhammadu Buhari, The Cable ta ce Femi Adesina ya tabo batun rashin lafiya.
Mai girma Buhari ya yi ta fama da jinya a lokacin da bai da lafiya, Adesina ya ce matsalar lafiyar ta taba tsohon shugaban sosai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Adesina a littafin, ya ce shugaba Buhari ya shaida masa cewa an kai lokacin da bai san a ina yake ba da ciwonsa ya yi kamari.
Shugaban Najeriyan tsakanin 2015 da 2023 ya shaidawa hadiminsa wannan lokacin da suka ziyarce shi a Landan a shekarar 2017.
Kamar yadda labari ya zo, Aisha Buhari tayi sanadiyyar da Adesina da sauran abokan aikinsa suka kawowa mai gidanta ziyara.
A littafin da aka kaddamar a makon jiya, marubucin ya ce wasu sun so shugaban kasar ya mutu a ofis sa'ilin da ciwo ya kama shi.
Vanguard ta rahoto Adesina yana cewa fastoci sun rika addu’a Buhari ya mutu a mulki, hakan zai ba Yemi Osinbajo damar gaje shi
Muhammadu Buhari ko Jibril daga Sudan
A Agustan 2021 da Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar waje, Adesina ya ce ya kara fahimtar farin jinin mai gidansu a Najeriya.
Jaridar ta rahoto tsohon mai magana da yawun shugaban na Najeriya yana cewa idan da Buhari zai sake yin takara, shi zai yi nasara.
Tsohon ‘dan jaridar ya ce bayan tafiyar ne wasu suka fara yada labari cewa ba Buhari ba ne a Aso Villa, wani Jibril aka kinkimo daga Sudan.
Littafin ya karyata masu wannan tunani na cewa mutumin da aka zaba a 2015 ya rasu.
Rayuwa bayan Buhari a Najeriya
Dazu aka rahoto majalisar NSCIA tana cewa a halin yanzu bukatun yau da gobe sun yi wa mafi yawan Musulman Najeriya wahala.
Malamai sun ankarar da gwamnati cewa adadin marasa hali yana cigaba da karuwa a cikin al’umma saboda cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng