Hadimin Buhari Ya Bayyana Abin da Aisha Ta Gaya Masa Lokacin da Ciwon Buhari Ya Tsananta

Hadimin Buhari Ya Bayyana Abin da Aisha Ta Gaya Masa Lokacin da Ciwon Buhari Ya Tsananta

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya bayyana abin da Aisha ta faɗa masa lokacin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke jinya
  • Adesina ya ce uwargidan tsohon shugaban ƙasar ta gaya masa cewa mijinta, Buhari, rashin lafiyarsa bai yi tsanani ba kamar yadda mutane ke zato
  • Ya bayyana cewa Aisha ta ce Buhari ya gaji ne kawai kuma aiki ya yi masa yawa, abin da yake buƙata shi ne hutu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hadimin tsohon shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya ce uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta gaya masa cewa mijinta, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, rashin lafiyarsa ba tsanani ya yi ba.

Kara karanta wannan

Adesina ya tuna da yadda Buhari ke ambatan sunan Yesu a sadda yake mulki

Adesina ya ce Aisha ta bayyana hakan ne a lokacin da shi da wasu mambobin majalisar ministoci suka kai wa Buhari ziyara, a birnin Landan na ƙasar Birtaniya a ranar 12 ga watan Agusta, 2017, cewar rahoton TheCable.

Adesina ya yi kan rashin lafiyar Buhari
Aisha ta ce Buhari hutu kawai yake bukata Hoto: Femi Adesina, Muhammadu Buhari, Aisha Buhari
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a cikin wani littafi mai suna, ‘Working with Buhari: Reflections of A Special Adviser, Media, and Publicity (2015-2023)’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Aisha ta ce kan ciwon Buhari?

Ya ƙara da cewa uwargidan tsohon shugaban ƙasar ta ce abin da kawai Buhari ke buƙata shi ne hutu domin ya gaji kuma aiki ya yi masa yawa.

A kalamansa:

"Wacce ta shirya ziyarar ita ce uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari. Jefi-jefi muke magana, amma a ranar da aka shirya tafiyar, wayata ta yi ƙara, ita ce. Bayan mun gaisa, sai ta ce: ‘Mijina ba ya rashin lafiya na ajali. Matsi ne kawai ya yi masa yawa. Tun shekarar da ta gabata nake gargaɗi a kai.

Kara karanta wannan

Badakalar N4bn: EFCC ta maka tsohon gwamna da tsohon shugaban PDP gaban kotu

"Abin da yake bukata shi ne hutu. Na yi kwana tara tare da shi, kafin na dawo don halartar wasu ayyukan mata. Yaran suna tare da shi.
"Ina ganin ya kamata kai ma ka ziyarce shi. Ba zai yiwu kana magana da yawunsa ba tare da ka ganshi ba.' A haka aka shirya ziyarar, bisa umurnin uwargidan shugaban ƙasa."

Showunmi Ya Faɗi Dalilin Ziyartar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa na hannun daman Atiku Abubakar, Segun Showunmi, ya bayyana dalilinsa na ziyartar Buhari a Daura.

Showunmi ya bayyana cewa ya ziyarci Buhari ne domin ya yi masa tambayoyi kan batutuwa da suka shafi gudanar da mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel