Ba Za Ta Yiwu ba: Dattawan Arewa Sun Soki Dauke Manyan Ofisoshi Daga Abuja Zuwa Legas

Ba Za Ta Yiwu ba: Dattawan Arewa Sun Soki Dauke Manyan Ofisoshi Daga Abuja Zuwa Legas

  • Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ba ta goyi bayan a maida wasu manyan ofishoshin tarayya zuwa Legas ba
  • Kakakin ACF na kasa, Tukur Muhammad-Baba ya ce akwai yunkurin karya gadon bayan yankin Arewacin Najeriya
  • Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar da wani dogon jawabi inda ya soki shirin da ake yi a FAAN da bankin CBN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Kungiyar ACF ta Dattawan Arewa ta soki shirin dauke hedikwatar hukumar FAAN daga birnin tarayya zuwa Legas.

Baya ga haka, jaridar Daily Trust ta ce kungiyar ba ta goyon bayan a dauke wasu manyan ofisoshin babban bankin CBN daga Abuja.

Bola Tinubu
Dattawan Arewa sun soki gwamnatin Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Facebook

ACF ta ce wannan yunkuri ba komai ba ne illa kokarin maida yankin Arewa saniyar ware.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin kakakin kungiyar dattawan Arewa

Sakataren yada labaran ACF na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya shaida haka a wani jawabi da ya fitar a karshen makon iya.

Kamar yadda Tukur Muhammad-Baba ya fada, mutanen yankin Arewa za a fi cuta a kokarin da ake yi na maida wasu ofisoshi zuwa Legas.

A jawabin na ta, kungiyar dattawan Arewacin Najeriyar ta zargi wasu a gwamnatin tarayya da karya Arewa da sauran bangarorin kasar.

Ba a ba 'Yan Arewa mukamai?

ACF ba ta karbi uzurin da aka bada na rashin isasshen wuri, rage kashe kudi da tsarin aiki wajen janye CBN da FAAN zuwa Legas ba.

"A ma’aikatar jiragen sama, darektoci 8 daga cikin 40 da aka nada ne kurum daga Arewa!"

- Farfesa Tukur Muhammad-Baba

Gwamnati za ta dauke aikin AVSATEL daga Katsina?

Daily Post tace ACF tayi ikirarin takarda ta fito daga AVSATEL da ke nuna za a janye aikin ARFF daga Katsina zuwa Kudu ko dai Abuja.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya kawo shawara da Pantami, mutane suka koma gayyar hada kudin fansa

Dattawan na Arewa sun yi ikirarin ana so maida aikin gyaran motocin kashe gobara a tashar jirgin sama zuwa Ibadan, Enugu ko Legas.

ACF tace an dade ana karya Arewa

A cewar ACF, da Olusegun Obasanjo ya karbi mulki, abin da ya fara shi ne maida hedikwatar NPA da NIIA zuwa Legas a maimakon Abuja.

Kungiyar tayi Allah-wadai da abin da ake yi wa Arewa tun daga kin yashe kogin Neja da Benuwai zuwa kin gyara tashoshin ruwa da wurin kiwo.

Shirin kai ofisoshin CBN Legas

Kwanaki an ji labari Kingsley Moghalu ya ce an gama ginin sabon ofishin Legas kuma an kaddamar da shi shekaru kusan 12 da suka wuce.

Adadin ma’aikatan da ke hedikwatar bankin CBN a Abuja sun yi yawa duba da lafiya da tsaron ginin don haka ya goyi bayan su koma Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng