Najeriya bazata rayu ba idan ba arewa – Kungiyar ACF

Najeriya bazata rayu ba idan ba arewa – Kungiyar ACF

Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Ibrahim Ahmadu Coomassie, ya bayyana cewa Najeriya bazata rayu ba idan babu arewa saboda haka ya zama wajibi akan shugabannin yankin da su ceto arewa daga ayyukan da zai nuna bakin ta.

Ya bayyana cewa ya zama dole a kawo karshen mumunan sahun da yankin ke ci gaba da bi tun bayan dawowar damokradiya a 1999.

Saboda haka, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari day a kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mata da yara da akeyi a yankin.

Najeriya bazata rayu ba idan ba arewa – Kungiyar ACF
Najeriya bazata rayu ba idan ba arewa – Kungiyar ACF

Shugaban kungiyar, Ibrahim Ahmadu Coomassie, ya bayyan a hakan a lokacin da shugaban kungiyar matan arewa, Jam’iyya Matan Arewa (JMA) suka ziyarci sakatriyan kungiyar na ACF a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Ko sama ko kasa: An nemi shaida an rasa a wajen sauraran karar Maryam Sanda

Coomassie wanda ya kasance tsohon sufeto janar na yan sanda yace Najeriya bazata rayu ba idan ba tare da arewa ba, don haka ya zama lallai shugabannin yankin su hada kawunansu domin ceto ta daga ayyukan da zai bata ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel