Yadda Tinubu Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro a Cikin Watanni 6 Inji Janarorin Soja

Yadda Tinubu Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro a Cikin Watanni 6 Inji Janarorin Soja

  • Wasu tsofaffin sojoji da suka kai matsayin Janar a bakin aiki, sun yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu
  • A matsayinsu na masana a harkar, sojojin sun kawo yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya
  • Idan shugaba Tinubu ya yi riko da shawarwarin da aka kawo, ana sai a samu zaman lafiya a 2024

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ganin kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ake yi ya yi yawa, sojojin tsofaffin sojoji sun ba gwamnatin tarayya shawara.

Vanguard ta rahoto tsofaffin sojojin suna bayanin abubuwan da ya dace ayi domin matsalar tsaro ta zama tarihi a kasar nan a bana.

Tinubu
Shugaban Najeriya yana fama da matsalar tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wadannan tsofaffin Janarori da takwarorinsu a gidan sojin sama da na kasa sun zanta da ‘yan jaridan a boye, ba a kama sunaye ba.

Kara karanta wannan

Ranar da jirgin Shugaban kasa ya kusa kifewa da Buhari da hadimansa a 2015

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuskuren Bola Tinubu a mulki

Wani tsohon soja ya ce daga cikin matsalolin da ake samu tun 1999 shi ne shugaban kasa yana bada umarni ba tare da tsaida lokaci ba.

Shiyasa yake ganin ya kamata ne Bola Tinubu ya ba minista da hafun tsaro da IGP wa’adin lokacin da yake bukatar a kawo zaman lafiya.

Sojoji su tsefe jejin 'yan ta'adda

Shi kuwa wani Janar mai ritaya cewa ya yi abin da ake bukata shi ne a rutsa miyagun da ke ta’adi, a hallaka su kaf ko a cafke su.

Sojan ya kawo shawarar shiga jejin Birnin Gwari, a tura sojojin yankin, a cewarsa idan aka yi haka, a watanni shida za a samu tsaro.

A hirar da jaridar tayi da wani tsohon jami’i, ya bukaci ayi koyi da salon da Janar Mohammed Marwa mai ritaya ya dauka a Legas.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

Marwa ya shiga duk wani lungu da sakon Legas, ya cafke ‘yan ta’ddan da suke barna.

Sojoji sun shiga aikin 'yan sanda?

Akwai wani tsohon sojan sama da ya ce an yi kuskure tun farko, ana ba sojoji aikin da ya kamata ya zama dakarun ‘yan sanda suke yi.

Sojan ya ce aiki ya yi wa sojoji yawa, ya kawo shawarar a samu hadin-gwiwar sojoji, NSCDC, ‘yan sanda, kwastam, NIS da sauransu.

Shi kuma wani Rear Admiral mai ritaya ya nuna ana bukatar jami’an da suka dace a mukamai, ya kuma nuna dole sai da kishin kasa.

A cewar wani wanda ya kai Air Vice Marshal a gidan soja, an yi kuskure da aka yi watsi da sarakuna da kuma kananan hukumomi.

Da aka tattauna da wani, sai ya ce wajibi gwamnati ta samar da wuraren da matasa za su rika karar da karfinsu, ko kuwa su rika ta’adi.

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan APC ya bayyana dalili 1 da zai hana yan Najeriya karanta littafin Buhari

Shugaba Tinubu ya tuno iyalin sojoji

Rahoto ya zo kwanaki cewa hakkokin sojojin da su ka mutu ko aka hallaka a filin daga zai fito bayan iyalansu sun fara dade da cire rai.

Shugaban hafsun sojoji, Janar Taoreed Lagbaja ya ce tun 2011 dangogin jami'an tsaro ke jiran kudin, yanzu Bola Tinubu ya amince a biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng