Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Buba Marwa a matsayin Shugaban NDLEA
- An nada Mohammed Buba Marwa mai shekaru 67 a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da nadin Marwa wanda yake haifaffen Adamawa
- Magoya bayan Shugaban kasar sun shiga wani yanayi da wannan nadin
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin sabon Darakta Janar na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).
Marwa ya kasane Shugaban kwamitin fadar Shugaban kasa kan yaki da miyagun kwayoyi.
Masu ruwa da tsaki dun jinjinawa aiki da rahoton kwamitin a karkashin kulawar Marwa.
KU KARANTA KUMA: Hotunan Buhari yana rabawa yara kudi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya,kalli abunda yan Nigeria ke kiran Shugaban kasar
A matsayin jagoran soji na Lagas, Marwa ya yi suna kan kafa Operation Sweep, wani shirin tsaro da ya taimaka wajen dawo da tsafta da da’a ga tsaro a cibiyar kasuwancin na Najeriya.
Magoya bayan shugaba Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress sun taya haifaffen dan Adamawan murnar nadin nasa ta shafin Twitter.
Wasu kuma na ta sharhi kan nadin tare da tunawa da aikin da Marwa yayi a baya da kuma yakinin cewa zai yi fiye da hakan a gaba.
Wasu kuma na ganin akwai son kai a nadin, zargin da ake yiwa gwamnatin Buhari.
KU KARANTA KUMA: Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
A wani labarin, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar zabe (INEC) mai ci, Sanata Kabiru Gaya ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudancin kasar ta samar da Shugaban kasar Najeriya na gaba.
Sanatan mai wakiltan Kano kudu ya bayyana cewa idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a 2023, zai zama rashin adalci idan arewa ta nemi kujerar Shugaban kasar kuma.
Ya yi martanin ne a wata hira da jaridar Daily Sun wanda aka wallafa a ranar Asabar, 16 ga watan Janairu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng