Al Qalam: An Samu Karin Bayani Kan Dalibai Mata Na Jami’ar Katsina da Aka Sace
- Jami'ar Musulunci ta Al Qalam da ke jihar Katsina, ta ce akwai dalibanta mata guda biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Litinin
- Sai dai jami'ar ta ce ba ta da cikakken bayani kan satar daliban kasancewar ba a cikin makarantar ne aka dauke su ba
- Rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da daliban ne a kan hanyarsu ta komawa makarantar daga jihar Niger
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Katsina - Jami'ar Al Qalam da ke jihar Katsina ta tabbatar da sace dalibanta mata guda biyu, tana mai cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama'a na jami'ar, Akilu A. Atiku, ta bayyana cewa tuni iyayen daliban suka tabbatar da sace 'yayan nasu.
Sai dai sanarwar ta yi nuni da cewa har yanzu babu wani cikakken bayani akan yadda aka sace daliban saboda ba a cikin makarantar ne aka dauke su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sace daliban a hanyarsu ta zuwa Katsina daga Niger
Sanarwar ta kuma ce shugaban makarantar Farfesa Nasiru Musa Yauri na iya bakin kokarinsa don ganin an samu mafita kan lamarin.
Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da daliban ne a ranar Litinin a kan hanyarsu ta zuwa Katsina daga jihar Niger domin ci gaba da karatu bayan hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Suna daga cikin fasinjojin da ke tafiya a cikin wata motar haya lokacin da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Kungiyar dalibai ta NANISS sun magantu kan sace daliban
Daliban da aka sace su ne Habiba Ango Shantali da Maryam Abubakar Musa, kuma sun fito daga karamar hukumar Borgu da ke jihar Niger, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Kungiyar daliban jihar Nigeria (NANISS) ta bakin shugaban ta na kasa, Gambo Idris Shehu, ta tabbatar da rahoton sace daliban.
Gambo Shehu ya ce Shantali ba aji biyu a jami'ar inda take karantar kimiyyar siyasa yayin da Musa ke aji hudu tana karantar kimiyyar kwayoyin halitta.
Fasto ya nemi mabiyansa su bashi albashinsu na Janairu 2024
A wani labarin na daban, wani malamin coci, Fasto Anosike ya yi ikirarin cewa Ubangiji zai saukar da albarka akan mabiyansa idan har suka bashi dukkan albashinsu na watan Janairu.
Fasto Anosike ya kuma jaddada cewa duk wanda bai samu albarkar Ubangiji kafin tsakiyar shekara ba, to zai mayar masa da kudin sa.
Asali: Legit.ng