Talakawa Ne Kadai Za Su Shiga Aljanna a Najeriya, Fitaccen Mawaki Ya Dira Kan Masu Asusun Banki
- Seun Kuti, fitaccen mawaki a Najeriya ya bayyana ra’ayinsa kan wadanda za su shiga aljanna a kasar bayan sun mutu
- Mawakin wanda ke bin addinin gargajiya ya ce mafi yawan ‘yan Najeriya talakawa za su tsallaka zuwa aljanna
- Ya ce duk masu asusun bankuna ba su yi imanin cewa Almasihu na zuwa ba, don haka ba za su shiga aljanna ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas – Fitaccen mawaki a Najeriya, Seun Kuti ya ce a tunaninsa talakawa ne kadai za su shiga aljanna.
Kuti ya ce mabiya addinan Musulunci da Kiristanci da ke da asusun bankuna ba za su tsira ba a lahira, cewar The Nation.
Mene Kuti ke cewa kan talakawa?
Ya bayyana haka ne inda ya ce mabiya addinai ba za su shiga aljanna ba saboda rashin amincewa Almasihu zai dawo shiyasa suke ajiye kudi don gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin wanda ke bin addinin gargajiya ya ce mafi yawan ‘yan Najeriya talakawa za su tsallaka zuwa aljanna.
Ya kara da cewa daga cikin wadanda suka mallaki asusun bankuna a cikin miliyan 200, wadanda ba su da shi ba su wuce miliyan 48 ba.
Maganarsa kan masu asusun banki
Ya ce:
“Lokacin da mutane ke kokarin yi min wa’azi cewa haba Seun ya kamata ka karbi Isa Almasihu, ina musu tambaya daya kacal.
“Shin kuna da asusun banki? Idan ka na da shi to dukkanmu daya ne, duk inda zan je idan na mutu, kai ma can za ka je.
“Saboda idan ba ka yadda Almasihu zai dawo ba, ba ka cika Kirista ba, amma da kuka ce kun yadda Almasihu zai dawo kuma kuna ajiye kudade don gobe ashe ba ku yi imani ba kenan.”
Kuti ya kara da cewa:
“Talakawa su kadai ne za su shiga aljanna wannan shi ne abin da ake nufi, ba masu asusun bankuna ba.
Ya ce mafi yawan masu shiga aljanna ‘yan Najeriya ne talakawa saboda sun cancanci hakan, cewar Daily Post.
Kotu ta umarci kama Malam Idris
A wani labarin, Kotun Shari'ar Musulunci ta umarci sake kama Sheikh Abdul'aziz Idris.
Kotun ta ba da umarnin ne bayan malamin ya ki amsa gayyatarta don ya gurfana a gabanta.
Asali: Legit.ng