Cece-kuce Yayin da Gwamna Kirista Ya Shiga Cikin Masallaci Sallar Juma'a da Tinubu, an Yada Bidiyon

Cece-kuce Yayin da Gwamna Kirista Ya Shiga Cikin Masallaci Sallar Juma'a da Tinubu, an Yada Bidiyon

  • An yi ta cece-kuce bayan gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya shiga masallacin Juma'a tare da shugaban kasa, Bola Tinubu
  • A ranar Alhamis ce 21 ga watan Disamba Shugaba Bola Tinubu ya dira a Legas don gudanar da bikin Kirsimeti
  • Gwamnan ya ci gaba da zama a masallacin tun daga farko har lokacin da aka kammala huduba da kuma sallar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - A ranar Alhamis ce 21 ga watan Disamba Shugaba Bola Tinubu ya dira a Legas don gudanar da bikin Kirsimeti.

Zuwan shugaban ya samu tarba mai kyau daga yaron dakinsa kuma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ni na taimaki APC ta ci mulki, gwamnan Arewa ya soki 'yan Majalisar Tarayya da Suka Sako Shi a Gaba

Dirama yayin da Tinubu ya shiga sallar Juma'ar da Gwamna Sanwo-Olu
Tinubu ya shiga sallar Juma'a da Gwamna Babajide Sanwo-Olu. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Twitter

Mene ya jawo cece-kuce kan ziyarar Tinubu Legas?

Sanwo-Olu ya kuma kasance tare da shugaban a duk inda zai je musamman wasu ayyuka ko wurin taro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da yafi daukar hankali shi ne lokacin da Tinubu ya je sallar Juma'a inda gwamnan wanda Kirista ne ya shiga masallacin tare da shi.

Sanwo-Olu ya kasance a cikin masallacin har zuwa lokacin da aka kammala sallar tare da shugaban kasar.

A ina Tinubu ya yi sallar Juma'ar?

Gwamnan ya zauna a can gefen masallacin inda har ya ke gyada kai alamun ya na sauraro kuma da fahimtar abin da ake fada.

Tinubu ya yi sallar Juma'ar ce a masallacin Ansar-Ud-Deen da ke jihar inda bayan kammala sallar al'ummar Musulmai suka tattauna da shugaban.

Tinubu ya mulki jihar daga shekarar 1999 zuwa 2007 inda ya daura wasu daga cikin yaran gidansa a kujerar gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

Musulmai sun yi wa gwamna Kirista addu'a

A wani labarin, Al'ummar Musulmai a birnin Jos da ke jihar Plateau sun Yi addu'a ma musamman ga gwamnan jihar.

Musulman wadanda su ka fito daga dukkan kananan hukumomi 17 sun karanta ayoyin Alkur'ani don samun nasarar Gwamna Caleb Mutfwang.

Daya daga cikin masu addu'ar ya bayyana cewa dalilin addu'ar shi ne don neman taimakon Allah ga gwamnatin Caleb wacce ba ta nuna wariyar addini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel