Miyetti Allah Ta Kaddamar da Kungiyar Yan Sa Kai Mai Mutane 1,144 Don Yakar Yan Bindiga a Nasarawa
- Kungiyar Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan sa kai don yakar 'yan bindiga da barayin shanu a jihar Nasarawa
- Kungiyar ta horas da mambobinta 1,114 wadanda za su yi aiki bisa tsarin doka tare da neman taimako daga jami'an tsaro
- Kungiyar ta kuma jaddada cewa ba duka Fulani makiyaya ne 'yan ta'adda ba, don haka ta gargadi mambobinta da su kauracewa shiga wata rigima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar nasarawa - Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan sa kai ta mutum 1,144 don yakar 'yan bindiga, barayin shanu, masu garkuwa, da 'yan ta'adda a jihar Nasarawa.
Da ya ke jawabi a garin Lafia yayin kaddamar da kungiyar, shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Bodejo ya ce sun zurfafa bincike kafin zabo mambobin kungiyar 'yan sa kan.
Ya ce 'yan sa kan za su yi aiki ne ta hanyar amfani da dokokin kasar Najeriya, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Ba duka Fulani ne 'yan ta'adda ba - Bodejo
Peoples Gazette ta ce ya nemi mambobin kungiyar 'yan sa kan da su hada kai da sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro yayin gudanar da ayyukan su a kananan hukumomi 13 na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Batu kan cewa Fulani 'yan ta'adda ne, Bodejo ya ce hakan ba gaskiya ba ne, sai dai ya nemi al'ummar Fulani da su zauna da kowa lafiya da kowa.
Ya ce duk wani bafullatani da ya tayar da tarzoma kuma jami'an tsaro suka kama shi ba zai samu agaji daga kungiyar ba, Leadership ta ruwaito.
Sojoji da 'yan sanda sun halarci taron Miyetti Allah
Ya ce:
"A cikin kowacce kabila, an samun wasu da ke bata sunan wannan kabilar, don haka bai kamata ayi wa Fulani kudin goro na cewa duka 'yan ta'adda ne ba.
"Ba mu samar da kungiyar 'yan sa kai na Fulani don nuna gazawar jami'an tsaro ba, mun yi hakan don karfafa masu guiwa da kara samar da tsaro a kasar baki daya."
Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa Umar Nadada, wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abdulaziz Aliyu ya jinjina wa kungiyar Fulanin na samar da 'yan sa kan.
Shi ma kwamandan bataliya ta 177 da ke Keffi, Lt. Col. Inuwa Bala ya nemi mambobin kungiyar 'yan sa kan da su bi dokokin da aka shimfida masu yayin gudanar da ayyukan su.
Yan bindiga sun kashe magidanci, sun sace yara 13 a hanyar Kaduna
A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun bugi kan wani magidanci mai suna Tijani Amedu, lamarin da ya yi silar mutuwarsa, kuma sun sace kananan yara 13 a hanyar Kaduna.
An ruwaito cewa Amedu da kananan yaran na hanyar zuwa Kaduna ne bayan dawowa daga garin Warri, jihar Delta, lokacin da 'yan bindigar suka bude wa motar su wuta.
Asali: Legit.ng