Babban Faston Najeriya Na Shirin Gina Katafaren Masallaci Na Miliyoyi a Wata Jiha
- Babban faston Najeriya, Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa ya kammala shiri tsaf don gina katafaren masallaci na miliyoyin naira a Legas
- Malamin addinin ya ce ya dauki wannan matakin ne don kawar da bambancin addini da nuna kaunar juna a cikin al'umma
- Primate Ayodele ya ce zai mika ragamar harkokin masallacin ga shugabannin Musulunci inda shi zai koma gefe ya zama dan kallo
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Ayodele, ya sanar da aniyarsa na gina katafaren masallaci na miliyoyin naira a jihar Legas.
Mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Osho Oluwatosin ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai, a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, Nigerian Tribune ta rahoto.
Dalilin da yasa zan gina masallaci, Fasto Ayodele
Fasto Ayodele wanda ya magantu kan shirin yin aikin masallacin tun a watan Disamba, ya ce bai yi hakan don wata manufa ta kashin kansa ba, sai don kawar da bambancin addini da nuna kaunar juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shahararren malamin addinin ya yi bayanin cewa Yesu Almasihu bai yi wa'azin addini ba sai na kyautatawa juna saboda haka, ba lallai sai mutum ya zama Kirista ko Musulmi ba, mu mutane ne kafin komai.
Primate Ayodele ya kuma bayyana cewa kasancewa mai kishin addini ba zai ba kowa damar shiga aljannah ba, rahoton The Eagle.
Sabanin haka, ya ce gudunmuwar mutum ga al'umma, zama tare da nuna kauna ga kowa ba tare da la'akari da bambance-bambancen ba shi ne babban addini.
Ya kuma bayyana cewa ba zai tsoma baki a harkokin Masallacin ba domin zai mika shi ga shugabannin musulmi bayan an kammala shi.
Faston ya kuma bayyana cewa ya tattauna sosai da shugabannin Musulunci kan wannan kudiri nasa na gina masallacin.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Fahimtar da Primate Ayodele ya yi wa addini bai taba zuwa da rabuwar kai ba.
"Ya sha bayyana cewa nuna soyayya ga kowa shine mafi girman addinin da kowa zai iya mallaka. Akwai musulmai da dama da suke bauta a cocinsa; har ma ana ba su damar sanya hijabi cikin harabar cocin.
“A lokacin azumi, al’adar Primate Ayodele ne rabawa al'ummar Musulmi da ke yankinsa kayan shayi, kaji masu rai, da kayan abinci.
"Don haka gina masallaci wani mataki ne na kara karya ginshikin bambancin addini."
Bukola Saraki ya gina masallaci
A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya bayyana wani kyakkyawan aikin da ya yi.
A cikin rubutun da ya yada a shafinsa na Facebook, Saraki ya bayyana cewa ya gina wani katafaren masallaci a garin Ilorin don cika alkawari.
A cewarsa, tun farko ya dauka wa mahaifinsa alkawarin gina masallaci, amma bai samu ya cika ba har sai da mahaifin nasa ya rasu.
Asali: Legit.ng