Sanatan APC Ya Sake Shiga Matsala Bayan Sarakuna 3 Sun Tona Masa Asiri, Gwamna Ya Yaba Musu
- Sanata Ifeanyi Ubah ya sake rasa mukamin sarauta bayan wasu sarakuna sun janye nadin nasu gare shi
- Igwe Onwuamaeze Damian da Igwe Gerald Obunadike dukkansu sun tube sanatan da ke wakiltar Anambra ta Kudu
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Charles Solude ya tube basarake kan ba da sarautar gargajiya ga Sanatan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra – Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan sarautar gargajiya ga Sanata Ifeanyi Ubah, masu sarauta uku sun sake tube sanatan.
Masu sarautar a kananan hukumomin Aguata da Anaocha da kuma Idemili ta Kudu dun sun janye sarautar da suka bai wa Ubah, cewar Punch.
Mene dalilin kwace sarautar?
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Charles Solude ya tube basarake kan ba da sarautar gargajiya ga Sanatan, cewar VON.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani mai sarautar gargajiyar ya nemi afuwar gwamnan wanda ya ba da sarautar cikin kuskure.
Igwe Onwuamaeze Damian da Igwe Gerald Obunadike dukkansu sun tube sanatan da ke wakiltar Anambra ta Kudu.
Wannan na kunshe ne a cikn wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Christina Aburime ya fitar a jiya Laraba 17 ga watan Janairu.
Mene gwamnan jihar ke cewa?
Masu sarautar gargajiya uku sun ba da sarautar gargajiyar ce ga Sanatan yayin bikin al’adu na Ofala a watan Disambar da ta wuce.
Ubah wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ya shirya tsayawa takarar gwamna da a shekarar 2025, cewar Daily Post.
Aburime a cikin sanarwar ya ce matakin da sarakunan suka dauka ya yi dai-dai da tsarin dokar masarautun a jihar.
Gwamna ya tube basarake kan ba da sarauta
A wani labarin, Gwamna Charles Soludo ya dauki mataki kan wani basarake bayan bai wa Sanata sarauta ba bisa ka’ida ba.
Igwe Eziani ya gamu da tsautsayin ne bayan bai wa Sanata Ifeanyi Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu sarauta a masarautarsa.
Daga bisani basaraken ya nemi afuwar Gwamna Soludo inda ya yi nadamar abin da ya aikata ba bisa tsarin dokar masarautu ba a jihar.
Asali: Legit.ng