"Wani Ya Dauka Yace Ta Mutu": Budurwa Ta Koka Yayin da 'Yar Uwarta Ta Bata Bayan Barin Makaranta

"Wani Ya Dauka Yace Ta Mutu": Budurwa Ta Koka Yayin da 'Yar Uwarta Ta Bata Bayan Barin Makaranta

  • An rahoto wata dalibar jami'ar Abuja, Halima, ta bata bayan ta fita zuwa makaranta
  • Danginta sun samu kira mai cike da damuwa daga wani da ba a san kowa nene ba ya na ikirarin cewa mai wayar ta mutu
  • Ba tare da sanin inda take ba, masoyanta na neman taimakon jama'a kan su taimaka a gano inda take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wata matashiya ta sanar da batun batar 'yar uwarta Mai suna Halima, wacce daliba ce a jami'ar Abuja.

'Yar uwar tata ta wallafa a shafinta na X cewa matashiyar bata dawo gida daga makaranta ba.

Budurwa ta koka bayan zargin kanwarta ta bace a hanyar zuwa makaranta
Budurwa ta sanar da batar kanwarta yayin da ta tafi makaranta. Hoto: GorgHerosa/TikTok.
Asali: Twitter

Batan Halima ya jefa 'yan uwanta cikin damuwa

Maganar karshe da 'yan uwanta suka yi da ita ya kasance da misalin karfe 3:00 na yamma, inda ta tambayi ko an gama abinci tare da tabbatar da shirinta na dawowa gida.

Kara karanta wannan

Kotu ta fara yanke hukunci kan shari'ar BBC da wani mawakin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya dauki sabon salo lokacin da wani ya amsa kiran wayar Halima da ayyana cewa mai wayar ta mutu.

Mutumin da ba a sani ba ya yi magana ne a harshen Hausa, kafin ya katse kiran.

Shiru ne ya biyo bayan duk wani kokari na sake kiranta, lamarin da ya jefa 'yan uwan Halima cikin damuwa game da halin da take ciki.

Mene 'yar uwar budurwar ke cewa?

'Yar uwar Halima ta rubuta cewa:

"Don Allah 'yar uwata ta bata, daliba ce a jami'ar Abuja, ta tafi makaranta yau, kasancewar ta kammala karatu a tsangayar injiniyar lantarki a karshen shekarar bara, don haka tana yin bincike ne da sauransu.
" Ta kira da misalin karfe 3:00 na yamma sannan ta ce tana hanyarta ta dawowa kuma ta tambayi ko an gama abinci tun daga sannan ba mu sake ji daga gareta ba har yanzu.

Kara karanta wannan

Dukiyar Aliko Dangote ta karu da sama da naira biliyan 510 a rana daya, an gano dalili

"Muna ta kiran lambarta sannan wani ya zo ya dauka ya ce mai wayar ta mutu, mai wayar nan ta mutu, sai ya fara magana a harshen Hausa sannan ya katse wayar, sai kuma suka daina daukar wayar don mu san a ina suke da sauransu.
" Mun kira mun kira sannan mun sake kira. Don Allah ku tayamu yadawa. Don Allah Ina rokonku ku duka. Idan kuna da labarin inda take don Allah ku taimaka mana. Sunanta Halima."

Yan uwan Halima sun matsu da son jin bayanin da zai iya taimakawa wajen gano inda Halima take da tabbatar da dawowarta lafiya.

Mahara sun kashe wasu mata a Abuja

A wani labarin, 'yan bindiga sun hallaka wasu uku daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da su a Abuja.

Wannan na zuwa ne yayin da yawan hare-haren 'yan bindiga ke kara yawa a birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng