Bayan Pantami Ya Dauki Mataki, Ministan Tinubu Ya Yi Gargadi Kan Kuskuren a Yakar Ta’addanci
- Gwamnatin Tarayya ta gargadi 'yan Najeriya kan tara kudaden fansa ga 'yan bindiga a kasar
- Badaru Abubakar, Ministan Tsaro shi ya bayyana haka a yau a Abuja yayin wani taro
- Ya ce yayin da gwamnatin ke cikin takaici kan 'yan bindigar, biyan kudaden zai kara bata lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gargadi matakin tara kudi don biyan kudaden fansa ga 'yan bindiga a kasar.
Ministan tsaro, Badaru Abubakar shi ya bayyana haka inda ya ce matakin zai kara rikirkita matsalar tsaro ne a kasar.
Mene Badaru ke cewa?
Badaru ya bayyana haka ne a yau Laraba 17 ga watan Janairu a Abuja yayin taron majalisar zartarwa, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya ce yayin da gwamnatin ke cikin takaici kan ayyukan 'yan bindigar, biyan kudaden zai kara ta'azzara tsaron ne.
Ya ce:
"Mun sani cewa biyan kudaden fansa ya harmata, babu yadda za a yi mutane su zo kafafen sadarwa su na neman a tara kudin fansa.
"Aikata hakan kawai zai kara ingiza matsalar ce wacce ake fama da ita a yanzu."
Wace shawara ya bayar?
Badaru ya bukaci 'yan Najeriya su guji kiraye-kirayen tara kudaden fansa ga 'yan bindiga a fili, cewar Vanguard.
Ya ce burin gwamnati shi ne kuntata musu musamman saboda ribar da su ke samu da ke kara ingiza su zuwa ga garkuwar.
Ya kara da cewa:
"Idan muka tsayar da ba da kudaden, yin garkuwar za ta zama babu riba, dole za su bari, abin babu sauki kam amma haka doka ta ce."
Wannan na zuwa ne bayan tsohon Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya ce ya samu wani daga abokansa zai biya miliyan 50 na kudin fansa.
Hakan ya biyo bayan garkuwa da wasu mata shida 'yan gida daya da aka yi wanda daga bisani suka hallaka Nabeena saboda kudin fansar.
Pantami ya bayyana takaici kan matsalar tsaro
A wani labarin, tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya bayyana takaici kan yadda tsaro ke kara kamari.
Pantami ya ce ya kawo tsarin da idan da ace an bi shi da yanzu an magance matsalar tsaron.
Asali: Legit.ng