Majalisa Tayi Karin N370bn a Ma’aikata 1, An Warewa Minista Naira Tiriliyan 1.03 a 2024
- Sanatoci da ‘Yan majalisar tarayya sun yi karin kudi a kan abin da aka warewa ma’aikatar ayyuka
- Majalisar Najeriya ta ga bukatar a kara adadin kudin da David Umahi zai kashe wajen yin hanyoyi
- Ministan zai kashe N1.03tr a madadin N657bn da Bola Tinubu ya gabatar a kundin kasafin na bana
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Majalisar tarayya tayi kari a kasafin kudin ma’aikatar ayyuka, abin da aka warewa ma’aikatar ya karu daga lissafin da aka yi.
Da farko N657.3bn Bola Ahmed Tinubu ya ware domin yin ayyuka a shekarar 2024, yanzu ‘yan majalisa sun kara kudin zuwa N1.03tn.
Majalisa tayi wa Minista karin 57%
Punch ta ce karin da aka yi ya kai N373bn ko a ce 56.7% na abin da aka ware a kundin da Bola Ahmed Tinubu ya mikawa majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin yana nufin kasafin kudin ma’aikatar ayyuka ya karu da 65.4% idan aka kamanta da kudin da aka warewa ma’aikatar a bara.
Aikin da Ministan zai yi a kasafin 2024
Wannan ma’aikata ce ta ke da alhakin gyara da kula da tituna na kilomita 33, 000 da ake da su da kuma gadojin da ke manyan hanyoyi.
A maimakon N617.9bn, jaridar ta ce ma’aikatar za ta batar da N987.3bn wajen yin ayyuka a sabuwar shekarar ta 2024 da aka shiga.
Takardar kasafin da aka samu ta nuna za a kashe N15bn wajen aikin titin Ota-Idiroko da kuma N4bn kan hanyar Iyin-Ilawe Ekiti a Ekiti.
An amince da N94.83bn domin gina titin Lafiya da fadada hanyar Otukpo-Makurdi.
Bangaren kwangilar titin Enugu-Fatakwal zai ci N13.5bn kamar yadda aka ware N10.1bn domin titin Malando-Garin-Baka-Ngaski-Wara.
Har ila yau a jihar ta Kebbi, kwangilar titin Koko-Besse-Zaria-Kala Kala za ta ci N11bn.
Ministoci sun koka da rashin kudi
Ministan ayyuka, David Umahi ya ce suna kokarin ganin an kammala aikin tituna na akalla kilomita 150 a kowace jiha a shekarar 2024.
Dama wasu ministocin kasar sun roki a kara yawan kudin da aka ware masu.
Akanta Janar a EFCC
Sababbin bayanai sun fito a wajen binciken tsohuwar Ministar jin-kai ta Najeriya, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu da aka dakatar.
Binciken ya jawo ana lalubo gaskiyar N3bn da aka taba a asusun COVID-19 a gwamnati, hakan ya sa aka kira Akanta Janar ta kasa.
Asali: Legit.ng