Bayan Ya Daidaita Kan Kujerar Mulki, Abba Kabir Ya Bayyana Abu 2 da Zai Fara Yaka a Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta shirya yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma kwacen waya a jihar
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin yaki da shan kwayoyi da kwacen waya ya fitar
- Hakan ya biyo bayan yawan kwacen waya da kuma rahoton da aka fitar kan ta'ammali da miyagun kwayoyi a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta gargadi masu ta’ammali da kwayoyi a jihar cewa a wannan karo ba za su ji da sauki ba.
Gwamnatin har ila yau, ta ce ta shirya saka kafar wando daya da masu kwacen waya a jihar wanda ya zama ruwan dare.
Mene kwamitin ke cewa kan matsalolin?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin yaki da shan kwayoyi da kwacen waya ya fitar, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bakin shugaban kwamitin, Burgediya Janar Gambo Mai'Adua mai ritaya ya bayyana shirinsu kan wannan matsala.
Mai'Adua ya ce a cikin rahoton da aka fitar cewa duk cikin mutane shida a jihar suna ta'ammali da kwaya abin takaici ne.
Ya ce dalilin haka gwamnatin jihar Kano ta shiga yaki da shan miyagun kwayoyi don tabbatar da an dakile harkar.
Ya kara da cewa kwamitin wanda Gwamna Abba Kabir ya kirkira a watan Octoban 2023 na aiki da wasu hukumomi don dakile shan kwayoyi.
A cewarsa:
"Yaki da wadannan matsaloli ba aikin gwamnati ba ne kadai, aiki ne na kowa da kowa a ko ina a fadin jihar.
"Idan muka yi saurin yakar matsalar shi ne abu mai kyau a cikin al'umma, sannan muna da kotun tafi da gidanka don yin shari'a a kan lokaci."
Matsalar kwacen waya a Kano
Shugaban kwamitin ya ce Abba Kabir ya shirya yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi da kwacen wayoyi har kwano a jihar.
Idan ba a mantaba, a daren ranar Lahadi ce wani mai kwacen waya ya fitar da makami tare da kwace wayar wata mata a birnin Kano.
Sai dai ya gamu da tsautsayi yayin da ya ke tsallaka hanya bayan mota ta murkushe shi nan take.
'Yan sanda sun kwashe shi zuwa asibiti inda daga bisani ya ce ga garinku bayan samun munanan raunuka a jikinsa.
An fara kiran mayar da Sunusi kujerarsa
A wani labarin, Bayan nasara a Kotun Koli, jama'ar Kano sun bijiro da maganar mayar da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi kujerarsa.
Magoya bayan Gwamna Abba Kabir sun yi shelar cewa 'Sabon Gwamna, Sabon Sarki' yayin da suka je tarar gwamnan.
Asali: Legit.ng