Kano: NDLEA Ta Yi Karin Haske Kan Cewa Duk ‘Dalibai 6 Cikin 10 Suna Shan Kwaya’

Kano: NDLEA Ta Yi Karin Haske Kan Cewa Duk ‘Dalibai 6 Cikin 10 Suna Shan Kwaya’

  • Hukumar NDLEA ta ce rahoton da wani jami'in ta ya fitar na cewa kaso 60% cikin 100% na daliban Kano na shan kwayoyi ba gaskiya ba ne
  • Kakakin NDLEA, Sadiq Maigatari ne ya yi karin haske kan wannan rahoto inda ya ce alkaluman da aka yi amfani da su ba wai na dalibai ba ne
  • Tun da fari ne babban sufeton NDLEA a Kano ya ce akwai bayani kan binciken da cibiyar ta yi da ya nuna kashi 60% na dalibai na shan muggan kwayoyi a Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta yi karin haske kan cewa dalibai shida cikin 10 da ke jihar suna shan miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Kano: Mota ta murkushe mai kwacen waya jim kadan bayan fauce wayar wata, ya shiga kakani-kayi

Babban Sufeton NDLEA na jihar, Jibril Ibrahim, ya bayyana cewa adadin masu shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai ya yi yawa kuma ana iya cewa ya haura kashi 50% cikin dari.

Rahoton hukumar NDLEA kan daliban jihar Kano.
Kano: NDLEA ta yi karin haske kan cewa duk ‘dalibai 6 cikin 10 suna shan kwaya’. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai da yake karin haske kan rahoton, kakakin NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce alkaluman sun ta'allaka ne kan daliban da aka yi musu magani a cibiyar gyaran halaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NDLEA ta ba daliban Kano hakuri

Dail Trust ta ruwaito Maigatari na cewa:

"Kididdigar kwanan nan da daya daga cikin ma’aikatanmu ya bayar game da shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai kuskure ne, kuma burinmu shi ne bayar da sahihan bayanai ga jama’a.
"Muna ba da hakuri ga duk wani rudani da wannan mummunar fassarar rahoton kididdigar ta haifar. Domin rahoto ne da ya shafi mutanen da aka yi wa gwaji a cibiyar ba wai duka dalibai ba."

Kara karanta wannan

APC ta sadaukar da kujerar gwamnan Kano ga Abba Kabir ne don gudun fitina? gaskiya ta fito

Ya ce suna sane da bayar da ingantattun bayanai ga jama'a, musamman idan ya zo ga batutuwa masu mahimmanci kamar amfani da miyagun kwayoyi, da harkar ilimi a jihar Kano.

Don haka ne ya ga cewar alhakinsu ne gyara duk wani rashin fahimtar bayani da aka samu da kuma tabbatar da cewa an yada sahihin bayanai kadai.

Yan sanda sun kama rikakken shugaban 'yan bindiga a Neja

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wani rikakken shugaban 'yan bindiga da ya addabi garuruwan jihar Neja da ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane.

Kwamishin 'yan sandan jihar Neja Shawulu Ebenezer Danmamman ne ya yi holen dan ta'addan mai suna 'Rabee', kuma ya ce sun kama shi a kasuwar Tungar Mallam da ke jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel