Tinubu Ya Fadi Halin Buhari 1 Da Ya Burge Shi, Ya Ce Ya Shammace Shi Bayan Barin Mulki

Tinubu Ya Fadi Halin Buhari 1 Da Ya Burge Shi, Ya Ce Ya Shammace Shi Bayan Barin Mulki

  • Shugaba Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan kammala wa'adinsa a gwamnati
  • Tinubu ya ce Buhari ya tsame kansa daga shiga harkokin gwamnatin musamman nadin Ministoci 48 da ya yi a watan Agustan 2023
  • Shugaban ya bayyana haka a yau Talata 16 ga watan Janairu yayin lancin din littafin Buhari a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan irin kau da kai da ya yi a gwamnatinsa.

Tinubu ya ce Buhari ya tsame kansa daga shiga harkokin gwamnatin musamman nadin Ministoci 48 da ya yi a watan Agustan 2023.

Tinubu ya yabawa Buhari kan rashin tsoma baki a gwamnatinsa
Tinubu ya yabawa Buhari bayan barin mulki. Hoto: Muhammadu buhari, Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Mene Tinubu ke cewa kan Buhari?

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan APC ya bayyana dalili 1 da zai hana yan Najeriya karanta littafin Buhari

Shugaban ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafin Buhari a yau Talata 16 ga watan Janairu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana abin da Buhari ya ce masa bayan mika mulki gare shi inda ya ce zai yi nisa har zuwa Daura sai dai idan ya na bukatar wani abu, cewar Channels TV.

Ya ce:

"Bayan mika mulki, Ka ce min za ka yi nisa har zuwa Daura, idan ina bukatar ka zan iya nemanka.
"Ba zan tsoma baki a harkokin ka ba, ba zan saka ido ba kuma ba zan yi shisshigi a harkokin ka ba.
"Mun hada kai don ganin dimukradiyya ta inganta da kuma samun ci gaba, Nagode sosai."

Wane yabo Tinubu ya yi kan Buhari?

Tinubu ya ce sai dai idan ya kira Buhari don ya ji ko ya na kan hanyar zuwa gona, idan ba haka ba, ba za ka taba jin labarin Buhari ba, Cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Daga yin kwana 7 har Tinubu ya shure umarnin da ya bada domin rage facakar kudi

Ya kara da cewa:

"Sai dai idan ni na kira shi, idan inason jin ko ya rayuwa ko kuma ya na tafiya gona ne.
"Idan ba haka ba za ka taba ji daga Buhari ba don cusa kansa a gwamnati ko wane korafi, nagode da yadda ka ke."

Tinubu ya yi magana kan garambawul a gwamnatinsa

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya yi fatali da jita-jitar cewa zai yi garambawul a gwamnatinsa musamman mukaman Ministoci.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin samun badakalar makudan kudade a ma'aikatar jin kai da walwala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.