Reno Omokri Ya Jero Manyan Dalilai 9 da Yasa Mulkin Tinubu Ya Fi Na Buhari

Reno Omokri Ya Jero Manyan Dalilai 9 da Yasa Mulkin Tinubu Ya Fi Na Buhari

FCT, Abuja - Hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya kwatanta mulkin Buhari da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Omokri wanda mai fashin baki ne a harkar siyasa ya jero dalilai 9 da ke nuna mulkin Tinubu ya fi na Buhari.

Reno Omokri ya bayyana dalilai 9 da ke nuna mulkin Tinubu ya fi na Buhari
Reno Omokri Ya Bayyana Dalilai 9 da Yasa Mulkin Tinubu Ya Fi Na Buhari. Hoto: Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Mutane da dama na yawan kwatanta gwamnatin Buhari da na Tinubu don sanin wane ya fi dama-dama a tsakani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hausa Legit ta leko abubuwan da Reno ya lissafo:

1. Tattalin arziki

Omokri ya ce Najeriya ta fuskanci matsalar tattalin arziki na tsawon shekaru 20 yayin da matsalar ta karu bayan hawan Buhari.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

Sai dai Omori ya ce an samu bunkasar tattalin arziki tun bayan hawan Tinubu saboda tsarte-tsarensa.

2. Kasuwancin masu hannun jari

Omokri ya ce a lokacin Buhari an samu matsala a bangaren zuba hannun jari yayin da a gwamnatin Tinubu kuwa aka samu ci gaba.

3. Kasuwar 'yan canji

Mai fashin bakin ya ce a mulkin Buhari, Bankin CBN ya na kashe dala biliyan 1.5 a ko wace wata don kokarin kare darajar naira.

Ya ce an samu sabanin haka a mulkin Tinubu yayin da ya kawo sabbin tsare-tsare a hada-hadar canji.

4. Yaki da cin hanci

Har ila yau, Omokri ya ce an samu badakalar makudan kudade a wurin Ministocin Buhari yayin da a mulkin Tinubu ya ke daukar matakin dakatar da su tare da fara bincike.

5. Sauyi a shige da ficen kasar

Ya bambance tsakanin mulkin Buhari da Tinubu yayin da ya ce ana samun matsalar samun Fasfo a mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo bayan Tinubu ya amince da manyan kudurori 3 da za su sauya rayuwar talaka a yau

Ya ce a yanzu Tinubu ya kawo tsarin bayar da Fasfo din cikin kankanin lokaci ta yanar gizo.

6. Tsare-tsaren Kirifto

A bangaren Kirifto, Omokri ya ce:

"Gwamnatin Buhari ta dakatar da harkokin Kirifto a kasar wanda ya jawo asarar dala tiriliyan 1.8 ga 'yan Najeriya.
"Tinubu ya dawo da martabar Kirifto inda ya janye dakatarwar wanda hakan ya bai wa matasan Najeriya damar samun kudaden shiga."

7. Gudanar da iyaka

Gwamnatin Buhari ta rufe iyaka inda ta sanya doka kan shigo da wasu kayayyaki da ya jawo tsadar kaya a kasar.

Omokri ya yabawa Tinubu inda ya ke daukar matakai don ganin ya kawo sauyi a bangaren da ya shafi iyakar kasar.

8. Wadatar man fetur

An sha samun matsalar karancin man fetur a lokacin mulkin Buhari a lokuta da dama musamman a karshen shekara.

Omokri ya ce sabanin haka aka samu a mulkin Tinubu yayin da aka fara inganta matatun mai a kasar tare da na Dangote.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

9. Harkar tsaro

A lokacin mulkin Buhari, sojoji sun shiga Zaria inda suka hallaka mutane 248 mafi yawanci 'yan Shi'a amma babu wanda aka hukunta.

Amma ya ce Tinubu na kokarin daukar mataki a duk lokacin da wani soja ya ci zarafin farar hula musamman abin da ya faru a Rivers.

Ya kara da cewa a zamanin Buhari 'yan bindiga sun hana mutane sakat kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, amma a yanzu zaka yi tafiya hankali a kwance.

Tinubu ya magantu kan garambawul a gwamnatinsa

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya yi martani kan jita-jitar cewa zai yi garambawul a gwamnatinsa.

Wannan na zuwa ne bayan samun zargin badakalar makudan kudade a ma'aikatar jin kai da walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel