Ekiti: Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Mamaye Babban Asibiti, Sun Sace Wata Gawa

Ekiti: Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Mamaye Babban Asibiti, Sun Sace Wata Gawa

  • A wani abu kamar almara, wasu 'yan daba sun farmaki asibitin Ekiti kuma sun yi awon gaba da wata gawa
  • Lamarin ya faru a safiyar ranar Litinin, inda 'yan dabar suka lalata kayayyakin da ke a sashin hadurra da ba da agajin gaggawa
  • Shugabannin asibitin da rundunar 'yan sanda sun gana da shugaban kungiyar matuka ta jihar don sun gano jagoran 'yan daban direba ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ekiti - Wasu 'yan daba sun mamaye asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ekiti da ke Ado Ekiti, kuma sun lalata kayayyaki a sashen hadurra da ba da agajin gaggawa biyo bayan mutuwar wani.

Yan daban wadanda suka fusata bayan mutuwar mutumin, sun sace gawar sa da karfin tsiya ba tare da sun bari an yi masa gwaje-gwaje ba.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

Yan daba sun sace gawa a Ekiti
Ekiti: ’Yan daba sun mamaye babban asibiti, sun sace wata gawa. Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Twitter

Shugaban asibitin, Farfesa Kayode Olabanji ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, inda ya yi Allah wadai da abin da 'yan daban suka aikata a safiyar ta Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sanda ta dauki matakin kariya a asibitin

Shugaban asibitin a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban hulda jama'a na asibitin, Rolake Adewumi, ya ce ba za su lamunci irin wannan aikin ta'addancin ba, The Nation ta ruwaito.

Olabanji ya ce shugabannin gudanarwar EKSUTH da 'yan sanda sun hadu da shugaban kungiyar direbobi ta jihar don nemo jagoran 'yan daban don sun gane direba ne.

Shugaban asibitin ya ce DPO da ke kula da ofishin 'yan sanda na Oke-Ila, SP Sesan Falade ya ba su tabbacin saka jami'an tsaro don yin rangadi akai akai a asibitin.

Dan daba ya taba kai farmaki sashen masu haihuwa

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Vanguard ta ruwaito shugaba asibitin na neman al'ummar asibitin da su kwantar da hankulan su domin sun dauki matakai na dakile irin faruwar hakan nan gaba.

Ya ce hukumar gudanarwar asibitin ba za ta ci gaba da zura ido ana cin zarafin ma'aikatan ta yayin da suke gudanar da ayyuka ba.

DPO Olabanji ya tariyo yadda wani dan daba ya taba shiga sashen masu haihuwa a asibitin, amma an kama shi kuma tuni yana gaban kotu yana jiran a yanke masa hukunci, cewar The Punch.

Yan bindiga sun kai wa sojoji farmaki a jihar Katsina

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai farmaki a wani sansanin sojoji da ke kauyen Nahuta a karamar hukumar Batsari, jihar Katsina.

An ruwaito cewa 'yan bindigar na dauke da muggan makamai, kuma sun farmaki kauyen Nahuta bayan kai wa sojojin hari, inda suka yi barna mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.