Hankula Sun Tashi Bayan Yan Bindiga Sun Halaka 4 Daga Cikin Mutum 10 da Suka Sace a Abuja

Hankula Sun Tashi Bayan Yan Bindiga Sun Halaka 4 Daga Cikin Mutum 10 da Suka Sace a Abuja

  • Birnin tarayya Abuja na fuskantar ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane yayin da wasu ɗalibai suka mutu a hannun waɗanda suka sace su
  • Rashin biyan kuɗaɗen fansar da ƴan bindigan suka nema ya sanya suka yanke shawarar halaka ɗaliban
  • Gano gawarwakin da aka yi ya sanya ƴan uwa da mazauna birnin tarayya Abuja sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A wani abu da za a iya kwatanta shi a matsayin wani lamari mai sosa zuciya, masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja, sun yi abin da ba a yi zato ba ga waɗanda suka sace.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƴan bindiga suka kashe mutum huɗu daga cikin mutum 10 da aka yi garkuwa da su a yankin Kubwa/Dutse tare da jefar da gawarwakinsu a Ida, kusa da Ushafa a ƙaramar hukumar Bwari.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya magantu kan sace shugaban karamar hukuma a jiharsa, ya aike da sako ga yan bindiga

Masu garkuwa da mutane sun tafka ta'asa a Abuja
Masu garkuwa da mutane sun halaka mutum hudu bayan kasa biyan kudin fansa a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Gawarwakin su waye aka gano?

Gawarwakin da aka gano sun haɗa da na wata ɗalibar sakandare, ɗiyar babban jami’in shari’a na hukumar NUC, Folorunsho Ariyo da ɗalibar jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, Nabeeeha Al-kadriyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi garkuwa da Folorunsho tare da mahaifiyarta da ƴan’uwanta uku a ranar Lahadi ta mako biyu da suka gabata, yayin da aka sace Nabeeeha Al-kadriyar tare da mahaifinta da ƴan uwanta mata biyar a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, cewar rahoton Daily Trust.

Gano gawarwakin mutanen da aka yi garkuwa da su, ya sanya iyalansu sun shiga cikin tashin hankali.

Majiyoyin iyalan sun shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa tun da farko masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓesu, inda suka buƙaci a biya su N60m, domin su sako iyalan Ariyo waɗanda suka kawai iya tara N5m.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani yayin da ƴan bindiga suka halaka Nabeeha a Abuja

Atiku Ya Yi Alhinin Kisan Nabeeha

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alhinin kisan da ƴan bindiga suka yi wa Nabeeha Al-kadriyar a Abuja.

Ƴan bindigan dai sun halaka Nabeeha ne bayan sun sace ta tare da ƴan uwanta da mahaifinsu a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng