Tsohon Sanata Ya Shiga Tashin Hankali Bayan ’Yan Damfara Sun Kwace WhatsApp Dinsa
- ‘Yan damfara sun datsi asusun wani tsohon sanatan Najeriya tare da yiwa abokansa wayo da kwace musu ‘yan kudade
- A ranar Asabar ne lamarin ya faru, inda sanatan ya daura laifin haka ga bankunan Najeriya da ke barin kafar sata a bankuna
- Ba wannan ne karon farko da ake haka ba a Najeriya, ya sha faruwa da mutane da yawa a yankuna daban-daban a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Legas - Abokan wani tsohon sanata a Najeriya, Tokunbo Afikuyomi sun tafka asarar miliyoyi yayin da wasu hatsabibai suka datsi manhajar WhatsApp din sanatan.
A rahoton da muka samo daga jaridar Punch, ya ce an yi rashin sa’a wasu sun datsi wayar tasa tare da tura sakwannin neman taimakon kudi ga abokansa.
A yayin da wasu suka yi wayon ankarar dashi a kan lokaci, wasu sun yi imani tare da tarar aradu da ka wajen tura kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki ya dauka?
A rahoton da ya aikewa jaridar, sanarwa ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar 13 ga watan Janairun da muke ciki.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sanatan ya gaggauta kai lamarin ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da an gano wadanda suka aikata wannan bakin aikin.
Hakazalika, ya mika sakon jimami da rashin dadin abin da ya faru ga dukkan wadanda suka gamu da wannan yaudara ta ‘yan damfara, rahoton The Cable.
Ya kushe bankunan Najeriya
A bangare guda, ya daura laifin aukuwar irin wannan yanayi ga bankunan kasar nan da ke kula da shige da ficen kudade kuma ya rataya a wuyansu.
Ya bayyana cewa, akwai rashin kwarewa da jajircewar bankunan wajen tabbatar da tsaro da kariya ga dukiyar al’umma.
Daga karshe, ya tura sakonsa ga wadanda suka taimaka wajen rage radadin damfarar ga wadanda abin ya faru, musamman gwamnan Legas da dai sauran jiga-jigan siyasar yankin.
Wani labarin damfara da ya hada da soja
A wani labarin, an ruwaito cewa wani dan damfara ta yanar gizo ya dauki hayan soja don farautar wani malamin addinin Musulunci mai suna Sulaimon a jihar Ogun.
Dan damfarar da ba a bayyana sunansa ba, na zargin malamin addinin da masa addu’a amma bai samu abin da ya ke nema ba a harkokinsa.
Mafi yawan ‘yan damfara na neman taimakon malaman addinai daban-daban da masu ba da maganin gargajiya da matsafa don cimma burinsu.
Asali: Legit.ng