Jimami Yayin da Mahara Suka Kona Fadar Babban Basarake Kurmus, Ya Koka Kan Lamarin

Jimami Yayin da Mahara Suka Kona Fadar Babban Basarake Kurmus, Ya Koka Kan Lamarin

  • Igwe Emmanuel Nnabuife ya shiga damuwa bayan mahara sun kone masa gida kurmus a kauyen Isseke a jihar Anambra
  • Mai sarautar gargajiyar a kauyen Isseke da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar, ya tabbatar da lamarin
  • Kamishinan ‘yan sanda a jihar, Aderemi Adeoye ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka an fara bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra – Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun bankawa gidan mai sarautar gargajiya wuta a jihar Anambra.

Mai sarautar gargajiyar a kauyen Isseke da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar, Igwe Emmanuel Nnabuife ya tabbatar da lamarin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane sun mutu yayin da motar gwamnati KTSTA ta yi mummunan hatsari, Gwamna ya magantu

Mahara sun kona gidan babban basarake a jihar Anambra
Mahara Sun Kona Gidan Babban Mai Sarautar Gargajiya a Anambra. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Yaushe aka kai harin?

Wannan na zuwa mako daya bayan ‘yan bindiga sun sace direban tsohon gwamnan jihar, Chinwoke Mbadinuju, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne yayin da ya ke gudanar da bikin binne dan uwansa da ya rasu a kauyen Isseke.

Rahotanni sun tabbatar cewa direban ya gagara biyansu kudaden su kafin binne dan uwan nasa inda suka farmaki gidansa da dare.

Maharan sun durfafi gidan nasa inda suka ta harbi a sararin samaniya yayin da suka dauke shi zuwa wani da ba a sani ba.

Mene basaraken ke cewa?

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Igwe Emmanuel Nnabuife ya ce maharan sun kona masa gidansa kurmus.

Ya koka kan yadda aka kai masa farmakin inda ya ce ba shi da matsala da kowa a yankin da za a yi masa haka, cewar Tori News.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Ya ce:

“Da gaske ne an kona mini gida kurmus wanda a yanzu haka na rasa komai da na sha wahalar nema a rayuwa, yanzu ba ni da gida.
“Komai ya kone amma nagode wa Allah babu rasa rai yayin lamarin da ya faru wanda ya tayar min da hankali.”

Kamishinan ‘yan sanda a jihar, Aderemi Adeoye ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka an fara bincike.

Yan sanda sun fitar da rahoto a Kano

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda da ke jihar Kano sun fitar da rahoto bayan yanke hukuncin Kotun Koli.

Wannan na zuwa ne bayan hasashen cewa za a iya samun tashin hankali a jihar kan hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel