Abin da Yan Bindiga Suka Fada Mana Kafin Mu Gano Gawar Nabeeha, Kawunta
- Wani kawun Nabeeha Al-Kadriyar, yarinyar da yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da ita da yan uwanta a Abuja ya magantu
- Sherifdeen Al-Kadriyar, ya ba da labarin yadda yan bindigar suka nemi su zo daukar sako wanda har ya kai su ga gano gawar Nabeeha
- Ya ce masu garkuwa da mutanen sun fusata ne a lokacin da iyalin suka sanar da su cewa rabin naira miliyan 60 da suka bukata suna iya hadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Sherifdeen Al-Kadriyar, kawun yarinyar da yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da ita da yan uwanta biyar a makon jiya a Abuja, ya bayyana yadda aka samu labarin rasuwar Nabeeha.
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda yan bindiga suka yi garkuwa da Nabeeha, mahaifinta da yan uwanta a yankin Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, a daren ranar Talata.
Yan bindigar sun bindige wani kawun marigayiyar, Alhaji Abdulfatai, wanda ya jagoranci yan sanda wajen ceto su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, biyu daga cikin jami'an yan sanda uku da harbin bindiga ya sama yayin musayar wuta sun ce ga garinku.
A cewar Trust Radio, kawun Nabeeha, wanda ke kokarin ganin an ceto yaran, ya ce yan bindigar sun fusata ne a lokacin da suka shaida musu cewa sun tara rabin kudin fansar na Naira miliyan 60.
A cewarsa:
"A ranar Juma'a wanda ita ce ranar da wa'adin da suka ba mu ya cika, sai suka kira sannan muka yi kokarin rokonsu da neman tattaunawa da su cewa mun iya tara kusan naira miliyan 30 ne.
"Bayan an kai ruwa rana, sai suka umurce mu da mu zo mu karbi wani sako a wani wuri da daddaren.
"Amma da muka isa wajen da misalin karfe 10:00 na dare, abun da muka gani ya girgiza mu. An yi wa Nabeeha da wasu mutum uku kisan gilla.
"Dole muka tafi da gawarmu tare da barin na sauran mutane uku wanda suma ga dukkan alamu na wadanda suka gaza cika yarjejeniya ne kuma muna da tabbacin su ma nasu mutanen nan nan zuwa."
Yan bindigar sun kara kudin fansar zuwa N100m
Sherifdeen ya kuma bayyana cewa sun sake kira daga baya sannan suka yi gargadin cewa za su dunga kashe sauran yan uwanta idan ba'a biya kudin fansar da suka kara zuwa miliyan 100 ba.
Kenan suna neman a biya naira miliyan 20 kan kowani mutum daya na sauran mutum biyar da suka rage zuwa ranar Laraba wanda shine wa'adi na gaba da suka bayar.
Ya kuma ce sun ki karbar naira miliyan 30 da suka kai masu. Haka kuma ya ce fushin da suka yi ya sa su zazzagi tare da yi masu barazana harda rokonsu kan su karbi miliyan 65 ko 70 wanda ba wai suna da shi ne ma.
Kawun nasu ya kuma roki gwamnatin jiha da ta tarayya da su kawo masu dauki don ceto sauran yara biyar da ke hannun yan bindigar don gudun kada abun da ya faru da Nabeeha ya ritsa da su.
Rundunar yan sanda ta yi martani
A halin da ake ciki, kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya jaddada cewar rundunar yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki kan lamarin ceto mutanen da aka sace.
Adejobi ya ce Kayode Egbetokun, Sufeto Janar na yan sanda ya yi umurnin fadada sashin tattara bayanan sirri domin yakar satar mutane.
Atiku ya yi martani kan rasuwar Nabeeha
Rasuwar Nabeeha ta haifar da ɓacin rai a shafukan sada zumunta musamman “X” (wanda aka fi sani Twitter a baya).
Da yake mayar da martani, Atiku ya bayyana matukar baƙin cikinsa kan rasuwar Nabeeha.
Asali: Legit.ng