Atiku Ya Yi Martani Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Halaka Nabeeha a Abuja
- A yayin da a ke juyayin kisan gillar da aka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar, Atiku Abubakar ya yi martani kan kisan da aka yi mata
- Martanin na Atiku Abubakar ya jaddada bukatar sake duba tsarin tsaron ƙasar nan cikin gaggawa domin daƙile ayyukan ta'addanci
- Nabeeha, ɗaliba ƴar 400L, ta gamu da ajalinta a hannun masu garkuwa da mutane, bayan sun sace ta tare da ƴan uwanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya mayar da martani kan rasuwar Nabeeha Al-Kadriyar.
Atiku Abubakar ya bayyana alhininsa kan rasuwar Nabeeha.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da ƴaƴansa shida, sun kashe ɗaya daga cikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindigan sun halaka Nabeeha ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.
Atiku ya yi martani kan rasuwar Nabeeha
Rasuwar Nabeeha ta haifar da ɓacin rai a shafukan sada zumunta musamman “X” (wanda aka fi sani Twitter a baya).
Da yake mayar da martani, Atiku ya bayyana matukar baƙin cikinsa kan rasuwar Nabeeha.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar a wani gajeren rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, @atiku a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu, 2024, ya buƙaci jami’an tsaro ciki har da ƴan sanda da su ƙara ƙaimi domin kuɓutar da ƴan uwan Nabeeha daga hannun masu garkuwa da mutanen.
Atiku ya rubuta a a shafinsa na Twitter cewa:
"Na ji baƙin ciki kan rahotannin kisan gillar da aka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar, wacce aka yi garkuwa da ita tare da ƴan uwanta, kuma ta shafe kusan makonni biyu a hannun waɗanda suka sace su."
"Wannan kuma wani abin tunatarwa ne cewa masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga suna gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarda ba a ƙasarmu, akwai bukatar a sake fasalin tsaro domin daƙile su ta yadda za a samu tsaron rayuka da dukiyoyi.
"Ya kamata jami'an tsaro su ƙara zage damtse domin ceto ragowar sauran waɗanda suke a hannun masu garkuwa da mutanen.
"Ina rokon Allah ya jikan marigayiyar da rahama ya kuma iyalanta haƙuri. - AA"
Atiku Ya Yi Jimamin Rasuwar Sheikh Giro
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi jimamin rasuwar Shiekh Giro Argungun.
Atiku ya ce Sheikh Giro na daga cikin manyan-manyan malaman addinin Musulunci da ake girmamawa a Najeriya da Yammacin Afrika baki daya, saboda irin gudummawar da ya ba da.
Asali: Legit.ng