“Ba Zan Iya Jurewa Ba Kuma”: Wata Soja Ta Fallasa Yadda Manyan Sojoji Ke Cin Zarafinta a Bidiyo
- Wata soja a rundunar sojin Najeriya ta zargi manyan jami'an sojoji da cin zarafinta tare da yi mata barazana da rayuwa saboda ta ki yarda da bukatarsu na yin badala da ita
- A cikin wani bidiyon TikTok da ya yadu, sojar ta yi zargin cewa an rufe ta, an koreta daga gidanta, sannan aka kai ta asibitin masu tabin hankali
- Sojar ta yi ikirarin cewa an daskarar da asusun ajiyarta na banki, sannan Kanar Abdulkareem daya daga cikin sojojin da ake zargi ya kawo mata cikas wajen ci gaban aikinta
- Sai dai kuma, rundunar sojin Najeriya ta bayyana aniyarta na gudanar da bincike a kan zargin tare da jaddada bukatar bin tsarin doka da oda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Wata jami'ar soja a rundunar sojin Najeriya ta koka a cikin wasu bidiyoyin TikTok da suka yadu, inda ta zargi wasu manyan jami'an soji da yi mata barazana da rayuwa saboda ta ki yarda da bukatarsu na lalata da ita.
Sojar, wacce ke amfani da shafin ogunleyeruthsavage1 a TikTok, ta ambaci sunan manyan jami'an sojin da Kanar IB Abdulkareem, Kanar GS Ogor da Birgediya Janar IB Solebo.
Ta ce jami’an na zaluntar ta tun bayan da aka tura ta asibitin sojoji na Ojo, Legas, a shekarar 2022, saboda ta ki yarda su yi lalata da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rufe ni sau da dama
Sojar ta ce an rufe ta sau da dama ba tare da wani dalili ba, aka kore ta daga gidanta, sannan aka rufe ta a asibitin mahaukata na tsawaon wata daya ba tare da wani bayanin likita ba tare da ikirarin cewa tana da lalurar kwakwalwa.
A cewar jami'ar sojar, an daskarar da asusun ajiyarta na banki tun a watan Fabrairun 2023 ba tare da albashi ba ko dalili ba.
Ta kuma yi zargin cewa Kanar Abdulkareem ya yi yunkurin yi mata fyade, amma da aka gano shi sai ya ce tana da tabin hankali.
Kalamanta:
"Idan wani abu ya same ni, don Allah a rike Kanar IB Abdulkareem, Kanar GS Ogor da Birgediya Janar IB Solebo, saboda basa so na girma. Ba sa son ci gabana.
"A shekarar 2022, an tura ni asibitin sojoji, Ojo inda na hadu da Kanar IB Abdulkareem, wanda ya neme ni amma na ki yarda.
"Tun daga lokacin, wannan mutumin ya zame mun mugun mafarki a rundunar soji yana barazanar korata a duk lokacin da ya gan ni."
Kanar Abdulkareem ya hana a yi mun karin girma
Sojar ta kuma yi zargin cewa Kanar Abdulkareem ya hana ta shiga duk wani kwas na sojoji tare da hana ta ganin iyayenta.
Ta ce a karshe da mahaifinta ya tuntubi Kanar Abdulkareem kan lamarinta, shi (Abdulkareem) ya fada ma mahaifinta cewa ya umurce ta da ta bi umurnin karshe da aka bata.
Ta ce "umarni na karshe" shine a bar Kanar din ya kwanta da ita.
Jama'a sun yi martani
MUSTAPHA ya ce:
"An kai matashiyar nan bango kuma ba ta da zabi. Yawancin sojoji mata na fuskantar irin haka."
Glory Francis ta ce:
"Don Allah ki yi hankali da abun da kike fadi idan kuna son barin rundunar soji ne ki bar shi ta hanyar da ta dace ta hanyar yin murabus."
Bradandgate ta ce:
"Idan har abun da take fadi gaskiya ne, wannan cin zarafi ne da ya kai kololuwa. Ya kamata a dauki mataki don gyara."
Chimaosuji ta ce:
"Kaiiiii babu banbanci tsakanin rundunar soji da na yan sanda yanzu. Abun tausayi ne cewa rundunar sojin Najeriya ta zama kamar aikin gwamnati."
An kama sojan bogi a Nasarawa
A wani labarin, mun ji cewa rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa sun ce sojojin Najeriya sun kama wani sojan gona a karamar hukumar Awe, inda suka mika shi ga rundunar don gudanar da bincike.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ya fitar da sanarwar hakan a ranar Alhamis a garin Lafia.
Asali: Legit.ng