Kayan sojoji mu ke karba haya idan zamu fita aiki - Mai garkuwa da mutane

Kayan sojoji mu ke karba haya idan zamu fita aiki - Mai garkuwa da mutane

Daya daga cikin wasu 'yan ta'adda uku da jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar kungiyar Fulani makiyaya (Miyetti Allah) suka kama a jihar Kano ya bayyana cewa suna amfani da kakin sojoji na gaske wajen gudanar da aikinsu.

Sai da jami'an 'yan sanda na atisayen 'Puff Adder' da hadin gwuiwar sauran jami'an tsaro da wakilan kungiyar Miyetti Allah ne suka hada gwuiwa kafin kama kama 'yan ta'addar uku; Lawan Mohammed, Sulaiman Abdullahi da Sai'du Abdullahi.

Jami'an tsaron na zargin Lawan da Sulaiman da laifin shatar shanu, yayin da shi kuma Sa'idu ake zarginsa da laifin satar mutane domin yin garkuwa da su. A yayin bajakolin masu laifin ne Sa'idu ya bayyana cewa da kayan sojoji ya ke amfani duk lokacin da zasu fita aiki.

DUBA WANNAN: Samun nasara a kotu: Buhari bai yi 'mi'ara koma baya' a kan furucinsa ba - Fadar shugaban kasa

An samu shanun sata fiye da 1,000 bayan jami'an tsaron na hadin gwuiwa sun samu nasarar cafke masu laifin a Kano.

Kazalika, an samu bindigu, alburusai da wasu kayan sojoji bayan an cafke mai garkuwa da mutane, Sai'idu. Wanda ake zargin ya bayyana cewa shugabanninsu ne ke karbo musu hayar kayan sojojo kuma su mayar da kayan ga sojojin bayan sun kammala amfani da su.

Sai dai, ya ce bai taba haduwa da jami'an sojojin da ake karbo kakinsu ba.

Kayan sojoji mu ke karba haya idan zamu fita aiki - Mai garkuwa da mutane
Lawan Mohammed, Sulaiman Abdullahi da Sai'du Abdullahi.
Asali: Twitter

Kayan sojoji mu ke karba haya idan zamu fita aiki - Mai garkuwa da mutane
An samu shanun sata fiye da 1,000 bayan jami'an tsaron na hadin gwuiwa sun samu nasarar cafke masu laifin a Kano
Asali: Twitter

Kayan sojoji mu ke karba haya idan zamu fita aiki - Mai garkuwa da mutane
Kayan sojojin da aka samu bayan kama Sa'idu, mai garkuwa da mutane
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel